Sojoji Sun Ceto Mutanen da Aka Gani a Bidiyo tare da Janar Rabe a hannun 'Yan Bindiga

Sojoji Sun Ceto Mutanen da Aka Gani a Bidiyo tare da Janar Rabe a hannun 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin Katsina ta sanar da ceto mutum hudu da aka gani tare da marigayi Janar Rabe Abubakar a wani bidiyo da ya yaɗu kwanakin baya
  • Dakarun Rundunar Sojin Najeriya ne suka ceto su yayin farmakin da suke kai wa maboyar ’yan bindiga a karamar hukumar Matazu
  • Gwamnatin Dikko Radda ta ce ana ci gaba da farautar fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Muhammadu Fulani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da nasarar da dakarun Sojin Najeriya suka samu na ceto mutum hudu da aka yi garkuwa da su daga hannun ’yan bindiga a jihar.

Gwamnatin ta bayyana cewa an ceto mutanen ne yayin ci gaba da farmakin da jami’an tsaro ke kai wa maboyar wani fitaccen ’dan bindiga da ake kira Kachalla Muhammadu Fulani da sauran mambobin kungiyarsa.

Kara karanta wannan

Dakarun gandun daji: Tinubu amince a dauki sababbin ma'aikata 1,000 a Katsina

Sojoji.
Dakarun sojoji tare da mutane 4 da suka ceto daga hannun yan bindiga a Katsina Hoto: Ibfahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Sojoji sun ceto mutum 4 a Katsina

Ta ce mutanen da aka ceton, wadanda shekarunsu ke tsakanin 36 zuwa 68, sun samu ’yancinsu ne bayan hare-haren soji da aka kai a wuraren da ake zargin ’yan bindigar suna boyewa, kamar yadda tashar Channels tv ta rahoto

Rahotanni sun nuna cewa mutanen da aka ceton sun samu raunukan harbin bindiga a lokacin da suke tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

Bayan ceto su, an garzaya da su asibiti domin samun kulawar lafiya cikin gaggawa kafin a sake had su da iyalinsu

Wannan nasara na zuwa ne makonni kadan bayan jami’an tsaro sun samu nasarar ceto matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar, Hajiya Amina Abubakar

Kara karanta wannan

Ana jimamin Janar Rabe, sarki ya sake mutuwa a hannun 'yan bindiga

Haka kuma, an bayyana cewa mutane hdu da aka ceton na daga cikin wadanda aka gani a wani bidiyo tare da marigayi Janar Rabe Abubakar yayin da suke tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

Gwamnatin Katsina ta yaba wa jami’an tsaro

A wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasir Mu’azu, ya fitar a ranar Laraba, ya yaba wa dakarun soji da sauran jami’an tsaro bisa jajircewa da kwarewar da suka nuna wajen gudanar da aikin.

Ya ce wannan nasara ta sake nuna kudurin jami’an tsaro na murkushe kungiyoyin masu aikata laifuffukan garkuwa da mutane da ta’addanci a fadin jihar.

Mu’azu ya tabbatar wa al’ummar jihar Katsina cewa jami’an tsaro na ci gaba da bibiyar Kachalla Muhammadu Fulani da sauran miyagu domin kamo su tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

Dikko Radda.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda a taron Majalisar zartarwa Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamnatin Katsina ta jaddada kudirinta

Kwamishinan ya sake jaddada kudirin gwamnatin Gwamna Dikko Umaru Radda na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsaro: An kafa zafafan dokoki a Katsina, an hana POS, cajin waya da sauransu

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro domin hana masu aikata laifuffuka samun mafaka a ko’ina cikin Katsina.

An tsaurara tsaro a makarantun Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa Sufeto Janar na Rundunar ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, ya umarci tsaurara tsaro a makarantun da ke fadin jihar Katsina.

Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da Sashen Kuɗi da Gudanarwa, Sulaiman Abdul, ne ya isar da saƙon ga rundunar yan sandan Katsina.

Ya ce an umurci rundunar da ta ƙara sintiri, ta inganta tattara bayanan sirri, sannan ta tabbatar da yawan bayyanar jami’an tsaro a kusa da makarantu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262