Gobara ta tashi a tsohuwar kasuwa a Sokoto
Hukumar kashe gobara ta jihar Sokoto ta tabbatar da barkewar gobara a tsohuwar kasuwa da ke Sokoto wacce ta kona shaguna 20.
Mista Mustapha Abubakar, Shugaban ayyuka a hukumar, ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Talata, 14 ga watan Janairu cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Litinin sannan ya ci gaba har zuwa karfe 2:00 na tsakar dare.
Abubakar ya bayyana cewa shagunan da lamarin ya shafa sun hada da na masu siyar da kayan kwaliyya da tufafin sawa, ina ya kara da cewa jami’ai sun kasance a wajen domin binciken abunda ya haddasa lamarin da barnar da ya yi.
Ya bayyana cewa za a bayar da cikakken rahoto kan lamarin.
Abubakar ya bayyana cewa masu kashe gobara sun yi kokari domin kawo karshen annobar duk tsawon daren.
Ya yaba ma mambobin kungiyar yan kasuwa da sauran hukumomi kan gudunmawar da suka bayar sannan ya yi addu’a kan kada Allah ya sa a sake samun afkuwar lamarin.
Ya kuma gargadi jama’a a kan kai rahoton gobara cikin kurarren lokaci.
Har ila yau ya yi gargadi kan toshe hanya yayin zairga-zirgan motocin kashe gobara a lokacin afkuwar lamarin.
KU KARANTA KUMA: Na siyar da kadarorin gwamnatin Kwara bisa ka’ida - Ahmed
Abubakar ya bayar da shawarar cewa kada mutane su bari sai sun sha fama da gobara kafin su sanar da hukumar, inda ya ce lamarin kan yi sanadiyar yaduwar wuta kafin zuwan masu kashe gobara.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng