Hankula sun tashi a Edo yayinda mutum 2 suka mutu a rikici tsakanin manoma a makiyaya

Hankula sun tashi a Edo yayinda mutum 2 suka mutu a rikici tsakanin manoma a makiyaya

Rahotanni sun kawo cewa mutane biyu sun mutu a wani karo tsakanin makiyaya da manoma a Sobe, karamar hukumar Owan ta yamma da ke jihar Edo.

Hakan ya haddasa tsoro da tashin hankali a zukatan al’umman Sobe kan yiwuwar harin ramuwa daga wajen makiyaya.

An tattaro cewa rikicin ya fara ne a ranar Lahi lokaci gawar wani dan shekara 11 an yanka shi a cikin wani daji.

An ruwaito cewa yaron ya je jeji ne domin ya samo ice lokacin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kashe shi.

Shaidu sun ce Yan uwan yaron daga yankin Kwale suka hadu sannan suka bi makiyayan inda suka kashe mutum daya daga cikinsu a yanayin.

KU KARANTA KUMA: Sanatocin Najeriya sun nuna fushi kan naira miliyan 2 da aka basu a matsayin goron Kirsimeti

Shugaban yankin, Mista Frank Ilaboya, wanda ya yi martani ga kisan ya roki al’umman yankin da su kwantar da hankalinsu.

Ilaboya ya ce ya sanar da kwamishinan yan sanda, CP Lawal Jimeta game da kisan sannan ya bukaci jami’an oka idan bukatar hakan ta taso.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel