Jika Ta Kashe Kakarta bayan Lakada Mata Duka, An Kashe Mai Shekara 96 da Tabarya a Katsina

Jika Ta Kashe Kakarta bayan Lakada Mata Duka, An Kashe Mai Shekara 96 da Tabarya a Katsina

  • Wata dattijuwa mai suna Hajiya Umma Husaini ta riga mu gidan gaskiya a jihar Katsina biyo bayan duka da aka ce wata jikar ta ce ta yi mata
  • Daya daga cikin 'ya'yan Hajiya Umma Husaini ya yi magana game da abin da ya faru tare da fadin wasu daga cikin halayen marigayiyar
  • Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina, DSP Sadik Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana matakin da suka dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Garin Daura a Arewacin jihar Katsina ya shiga jimami mai tsanani a ranar Asabar bayan kisan wata tsohuwa mai shekaru 96 mai suna Umma Husaini.

A cewar wasu majiyoyi da dama, an ce jikarta mai suna Aisha Muktar ce ta kai mata hari ta hanyar bugunta da turmi a cikin gidansu da sanyin safiyar ranar Asabar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Tsaro: An kafa zafafan dokoki a Katsina, an hana POS, cajin waya da sauransu

Taswirar jihar Katsina.
Taswirar jihar Katsina a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Halin da aka samu dattijuwa mai shekara 96

Majiyoyin sun shaida wa Daily Trust cewa maƙwabta da 'yan uwa da suka garzaya wurin sun tarar da Hajiya Umma kwance cikin jini, ba ta cikin hayyacinta kuma tana samu munanan raunuka.

Da suka ga halin da take ciki, nan take suka garzaya da ita zuwa cibiyar kiwon lafiya ta Tarayya da ke Daura domin samun kulawar gaggawa.

Majiyar ta ce:

“Jini na zuba sosai daga jikinta lokacin da muka isa,”
“Nan take muka ɗauke ta zuwa asibiti domin ceton rayuwarta.”

Kara karanta wannan

Yadda aka karbo gawar Manjo Janar Rabe Abubakar bayan ya rasu a hannun 'yan Bindiga

Duk da ƙoƙarin da ma’aikatan lafiya suka yi, an tabbatar da mutuwar tsohuwar bayan wasu sa’o’i kaɗan, lamarin da ya jefa iyalanta da al’ummar Daura cikin alhini.

Maganar ɗan matar da aka kashe

Da yake magana da manema labarai, babban ɗan marigayiyar, Muktar Husaini, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana kisan a matsayin abin takaici kuma wanda ba a taɓa tsammani ba.

Ɗan marigayiyar ya ce:

“Gaskiya ne an kai wa mahaifiyata hari kuma daga baya ta rasu a asibiti,”
“Dukkanmu muna cikin firgici saboda ba ta taɓa samun wata matsala da kowa a Daura ba.”

Muktar ya kuma bayyana marigayiyar a matsayin mace mai son zaman lafiya da tawali’u wadda ta sadaukar da rayuwarta wajen kula da iyalanta da kuma kyakkyawar mu’amala da maƙwabta.

Kara karanta wannan

"Ba ciwon sukari ba ne": Yaron Janar Rabe ya fallasa abin da ya yi zargin ya kashe mahaifinsa

Sufeton 'yan sandan Najeriya
Sufeton 'yan sanda na kasa, Tunji Disu a ofis. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

A cewar danginta, Hajiya Umma ta shafe shekaru da dama tana fama da ciwon sukari wanda daga ƙarshe ya kai ga yanke ƙafafunta biyu.

'Yan sandan sun magantu

Kakakin 'yan sanda a jihar Katsina, DSP Sadik Aliyu, ya bayyana cewa an tsare wadda ake zargi, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma dalilin harin.

Rahoton Trust Radio ya nuna cewa azauna yankin sun yi Allah-wadai da kisan tare da kira da a tabbatar an yi adalci, suna roƙon hukumomi su gudanar da cikakken bincike mai gaskiya.

Bayani kan matsalolin Arewa

A wani labarin, kun ji cewa shugaban gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi magana kan matsalolin da suka addabi yankin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa fadar sarki da dare, sun bindige matarsa bayan garkuwa da shi

Inuwa Yahaya ya bayyana cewa matsalolin talauci, jahilci, rashin aikin yi da tabarbarewar tarbiyya sun ƙaru a yankin Arewacin Najeriya tsawon shekaru.

Gombe Jihar Gombe ya bukaci shugabannin siyasa, gargajiya da na addini su tashi tsaye domin kawo karshen matsalolin su maimakon yawan surutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng