Sanatocin Najeriya sun nuna fushi kan naira miliyan 2 da aka basu a matsayin goron Kirsimeti

Sanatocin Najeriya sun nuna fushi kan naira miliyan 2 da aka basu a matsayin goron Kirsimeti

Rahotanni sun kawo cewa sanatocin sun nuna fushinsu a kan naira miliyan biyu da aka ba kowannensu a matsayin goron Kirsimeti.

Harma an jiyo wasu sanatoci na bayyana kudin da aka basu a matsayin digo cikin tarin bukatunsu na Kirsimeti.

Jaridar Premium Times ta ruwaitoc cewa lamarin ya kai har wasun su na barazanar sanyawa Shugaban majalisar dattawan ciwon kai daga dawowarsu ddaga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara a wannan watan.

“Basu isa daukar nauyin dukkanin bukatunmu na Kirsimeti ba,” inji wani sanata. “A halin yanzu ma, wasun mu sun hadu domin yiwa shugabanmu korafi.”

Yan majalisan sun samu naira miliyan biyu kowannensu a ranar 18 ga watan Disamba daga asusun majalisar dattawa kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

A cewar daya daga cikin sanatocin da suka yi magana bisa sharadin boye sunansu ya ce suna iya fallasa korafinsu a bainar jama’a idan har aka hofantar da fushinsu.

KU KARANTA KUMA: Marasa zuwa Makaranta a Jihar Kano sun ragu da mutum kusan 1,000,000

“Sun ce muyi amfani da kudin wajen kula da iyalanmu da mazabunmu," inji wani sanata. “Kawai tsayawa nayi a wajen ba tare da na san abun fadi ba na tsawon wasu mintuna.”

Sanatan ya koka cewa Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan ya gaza fahimtar irin nauyin da kan tunkaresu a duk lokacin da suka ziyarci mazabunsu.

Yayinda sanatocin sun gaza fadin nawa ya kamata su samu a matsayin goron Kirsimeti, sun nuna yakinin cewa abunda ya kamata kowani mamba na majalisar mai mutane 109 ya kamata ya samu ya fi naira miliyan biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel