'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Cibiyar NIPSS a Plateau, an Kashe Mutane

'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Cibiyar NIPSS a Plateau, an Kashe Mutane

  • 'Yan bindiga sun kai wani hari a cibiyar bincike kan manufofi da tsare-tsare ta kasa (NIPSS) da ke Kuru a jihar Plateau
  • Hatsabiban 'yan bindigan dauke da makamai sun farmaki cibiya ne cikin dare inda suka yi musayar wuta da jami'an bayan sun kai harin
  • Shaidun ganau ba jiyau ba sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe mutane ciki har da jami'an tsaro yayin harin da suka kawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Wasu 'yan bindiga sun farmaki cibiyar bincike kan manufofi da tsare-tsare ta ƙasa (NIPSS) da ke Kuru, kusa da Jos, a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun kashe mutane uku, ciki har da wani ɗan sanda yayin harin da suka kai a cibiyar ta NIPSS a jihar Plateau.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar The Punch ta ce a cewar shaidun gani da ido, maharan sun mamaye cibiyar ne da misalin ƙarfe 11:40 na daren ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Neja, an kashe mutane da kona gidaje

'Yan bindiga sun farmaki NIPSS

Shaidun sun bayyana cewa 'yan sun buɗe wa jami'an tsaron da ke gadin ƙofar cibiyar wuta, wanda hakan ya haifar da musayar wuta da jami'an tsaron da aka tura cibiyar.

Wani ma'aikacin NIPSS, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da aukuwar harin a Jos ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2026, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Ya bayyana cewa:

“Ina barci na ji ƙarar harbe-harben bindiga. Ban san abin da zan fassara hakan da shi ba, amma lokacin da na tashi, na gano cewa da gaske ne domin harbe-harben sun riga sun haifar da hargitsi a cikin NIPSS. Sai ya zama ashe cibiyar ce ake kai wa hari.”

Jami'an tsaro sun fafata da 'yan bindiga

Majiyar ta tabbatar da cewa jami'an tsaro sun fafata da maharan a wata zazzafar arangama domin hana su samun damar shiga cikin cibiyar.

“Godiya ta tabbata ga Allah da aka ƙara turo jami'an tsaro, kuma maharan sun tsere. Amma sun yi nasarar kashe mutane biyu a ƙofar gida kafin su gudu. Wani soja da ɗan sanda ne abin ya shafa. Abin takaici ne kwarai."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari a Kebbi, an kashe bayin Allah

"Mutane uku ne suka rasa rayukansu a lokacin harin, ciki har da wani ɗan sanda da kuma wani jami'in da ke aiki a sashen tsaron cibiyar.” Inji majiyar
'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa saurin mayar da martani na jami'an tsaro ya hana 'yan bindigar ratsawa zuwa cikin cibiyar da kuma yin ƙarin ɓarna.

Bulus Haruna, wani mazaunin Kuru a karamar hukumar Jos ta Kudu, ya bayyana cewa mazauna garuruwan da ke kewaye sun shiga cikin fargaba biyo bayan jin ƙarar harbin bindiga da aka kwashe mintuna da dama ana yi.

'Yan bindiga sun saka harajin noma a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kakaba haraji ga mazauna wasu kauyuka 26 a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Harajin da 'yan ta'addan suka sanya ya zo ne bayan hana mutanen yankunan zuwa gonakinsu yayin da ake shirin fara noman damina.

‘Yan bindigan sun yi barazanar kashewa ko sace duk wanda aka samu yana noma daga cikin mazauna kauyukan da abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng