Diezani: Kotu Ta Wanke Tsohuwar Ministar Najeriya daga Zargin Karbar Rashawa

Diezani: Kotu Ta Wanke Tsohuwar Ministar Najeriya daga Zargin Karbar Rashawa

  • Alƙalan kotu a Birtaniya sun wanke tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, daga dukkan tuhume-tuhumen rashawa
  • Rahoto ya nuna cewa, wata shaida da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya aike wa kotun ta taka muhimmiyar rawa a wanke Diezani
  • Tun da fari, hukumomin Birtaniya sun zargi Diezani da karɓar kyaututtuka da kadarori masu tsada da nufin su yi tasiri wajen bayar da kwangilolin mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Birtaniya — Kotun Southwark Crown da ke birnin Landan ta wanke tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, daga dukkan tuhume-tuhumen rashawa.

Rahotanni sun nuna cewa alƙalan kotun sun yanke hukuncin ne bayan sun shafe sama da sa’o’i 46 suna nazari kan hujjojin da aka gabatar a shari’ar.

Kotu a Birtaniya ta wanke Diezani Alison Madueke daga dukkan zarge zarge.
Diezani Alison-Madueke ta isa kotu don ci gaba da sauraron shari'ar zargin rashawa a London. Hoto: Henry NICHOLLS / AFP via Getty Images
Source: Facebook

Jonathan ya kare Diezani a kotu

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi, shugabannin Kirista sun yi kira da murya daya kan matsalar tsaro

An ce an wanke Diezani daga tuhume-tuhume shida da suka shafi zargin karɓar rashawa yayin da take jagorantar ma’aikatar man fetur ta Najeriya, in ji rahoton Reuters.

A yayin sauraron ƙarar, kotun ta karanta rubutacciyar shaidar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan da ya aike wa kotun.

A cikin bayanin nasa, Jonathan ya ce ba sabon abu ba ne wasu mutane ko hukumomi su biya kuɗin tafiye-tafiye a madadin ministoci idan suna gudanar da ayyukan gwamnati a ƙasashen waje.

Ya kuma bayyana cewa ya amince da amfani da jiragen haya masu zaman kansu da Diezani ta yi a wasu daga cikin tafiye-tafiyenta na aiki.

Yadda aka fara shari'ar Diezani

A farkon shekarar 2026 ne aka fara sauraron shari’ar bayan hukumomin Birtaniya sun gurfanar da Diezani kan zarge-zargen da suka shafi karɓar rashawa.

Tun a watan Agustan 2023 ne Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka ta Birtaniya ta fara gurfanar da ita bisa zargin karɓar cin hanci domin ba wasu kamfanoni damar samun manyan kwangilolin mai da iskar gas.

An kuma gurfanar da wasu mutane biyu tare da ita, ciki har da wani jami’in kamfanin mai da kuma ɗan uwanta, inda dukkansu suka musanta aikata laifin.

Kara karanta wannan

An yanke wa Hauwa'u Mukhtar hukuncin kisa, za a rataye ta a Katsina kan ta'addanci

Masu gabatar da ƙara sun yi iƙirarin cewa Diezani ta amfana da gidaje masu tsada, kayayyakin alatu da sauran fa’idodi daga wasu masu ruwa da tsaki a harkar mai.

Sun ce waɗannan mutane sun yi hakan ne saboda suna ganin za ta iya amfani da matsayinta wajen taimaka musu samun kwangiloli a fannin mai da gas, in ji rahoton The Cable.

Martanin lauyoyin Diezani a kotu

Lauyoyin Diezani sun musanta dukkan zarge-zargen da aka yi mata, suna masu cewa ikon amincewa da kwangilolin mai ba ya hannunta kai tsaye.

Sun bayyana cewa tsarin bayar da kwangiloli a fannin man fetur yana bi ta matakai da hukumomi daban-daban kafin ya isa ofishin minista.

A cewarsu, yawancin ikon gudanar da harkokin yau da kullum na masana’antar mai yana hannun shugabannin kamfanin man fetur na ƙasa, yayin da ma’aikatar ke taka rawar sa ido da tsara manufofi.

Kotu ta ce babu wasu gamsassun hujjoji da suka nuna cewa Diezani ta karbi rashawa.
Tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya Diezani Alison Madueke a taron OPEC 2021. Hoto: DIETER NAGL/AFP via Getty Images
Source: Twitter

Kotun ta wanke Diezani daga zargi

Bayan kammala sauraron shari’ar da nazarin hujjoji daga ɓangarorin biyu, alƙalan kotun suka yanke hukuncin cewa babu isassun hujjojin da za su tabbatar da laifukan da ake zargin Diezani da aikatawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shari'ar daruruwan wasu da ake zargi da ta'addanci

Saboda haka, kotun ta sallame ta tare da wanke ta daga dukkan tuhume-tuhumen da ake yi mata.

An fara gwanjon kadarorin Diezani

A wani labari, mun ruwaito cewa, EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa tayi kira ga mutane su nemi sayen kayan da gwamnati ta karbe.

Rahotannin da aka samu sun nuna cewa kayan da gwamnatin tarayya ta karbe su na garuruwan Legas, Ribas, Anambra, Gombe da Delta.

Har ila yau an karbe kaya daga ‘yan siyasa daga ‘yan kasuwa a jihohin Ebonyi, Kaduna, Delta, Edo, Kwara, Kuros Riba, Osun, Oyo da birnin Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com