An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Ayyana Wani Shirin Watanni 6 don Magance Matsalolin Najeriya

An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Ayyana Wani Shirin Watanni 6 don Magance Matsalolin Najeriya

  • Yan majalisar wakilai na jam'iyyun adawa sun ba da shawara kan yadda ya kamata gwamnatin tarayya ta tunkari matsalolin Najeriya
  • Sun bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana wani shiri na watanni shida domin dawo da zaman lafiya da walwalar jama'a
  • Yan adawar sun kuma nuna damuwarsu kan mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya a hannun 'yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsagin marasa rinjaye a Majalisar Wakilai ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana wani shiri na musamman na watanni shida domin magance matsalolin tsaro da tattalin arziki a Najeriya.

Sun ce kasar na fuskantar matsaloli da dama da suka hada da kashe-kashen rayuka, garkuwa da mutane, matsin rayuwa da kuma abin da ya kira yunkurin raunana jam’iyyun adawa kafin babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Zabe ne a gabansa': Yan majalisa sun dura kan Tinubu game da tsaron ƙasa

Majalisa.
Yan majalisar wakilai na tsakiyar zama a zauren majalisar tarayya Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Shugaban tsagin marasa rinjaye a majalisar wakilai, Hon. Fred Agbedi, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Yan adawa sunn dura kan Tinubu

Ya kuma zargi Shugaba Bola Tinubu da mayar da hankali kan siyasar neman tazarce a zaben 2027 da ke tafe maimakon kare rayukan jam'a da inganta walwalar ’yan Najeriya.

Dan Majalisar wakilan ya ce:

"Ya kamata Shugaba Tinubu ya dakatar da duk wata siyasar 2027 sannan ya ayyana shirin watanni shida na dawo da tsaro da farfado da tattalin arziki. Ya jagoranci kasa ko kuma ya yi murabus."

Mutuwar Janar Rabe ta ja hankali

Agbedi, wanda wasu ’yan majalisar suka raka yayin taron manema labarai, ya bayyana mutuwar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya a hannun masu garkuwa da mutane a matsayin abin kunya ga kasa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ware rukunin 'yan bindigan da zai yi sulhu da su idan ya zama shugaban kasa a 2027

Ya ce rasuwar tsohon babban jami’in sojan ta nuna yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa tare da haifar da tambayoyi kan lafiyar talakawan Najeriya.

"Idan har janar ba shi da tsaro a cikin kasarsa, wa ne zai ce yana da tsaro?" ya tambaya.
Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Sun nemi a ceto daliban Oyo

Dan majalisar ya kuma yi Allah-wadai da ci gaba da tsare dalibai da malamansu da aka sace a Jihar Oyo.

Ya zargi gwamnati da gazawa wajen daukar matakan gaggawa domin kawo karshen sace-sacen mutane, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Hon. Agbedi ya bukaci a kaddamar da wani farmakin soji na musamman domin ceto wadanda aka sace cikin sa’o’i 72.

Majalisa ta amince da yan sandan jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar wakilai ta amince da kudirin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi bayan kuri’ar da ‘yan majalisa 288 suka kada a makon da ya gabata.

An gudanar da kada kuri’ar ne ta hanyar daga hannu, inda kusan ‘yan majalisa 288 suka goyi bayan kudirin yayin da mutum hudu kacal suka nuna adawa da shi.

Sabon kudurin zai bai wa Majalisar tarayya damar tsara yadda rundunar ‘yan sandan tarayya za ta kasance tare da shimfida ka’idojin kafa ‘yan sandan jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262