'Yan Kasuwa Sun Fadi Sabon Farashin Fetur mai Sauki da zai Samu a Najeriya

'Yan Kasuwa Sun Fadi Sabon Farashin Fetur mai Sauki da zai Samu a Najeriya

  • Rahotanni sun nuna cewa a wannan makon ne matatar Dangote ta rage farashin litar fetur daga N1,250 zuwa N1,175 ga 'yan kasuwa
  • Sauke farashin ya sanya masana sun fara hasashen cewa farashin fetur a gidajen mai zai iya sauka zuwa tsakanin N1,200 da N1,250
  • Duk da cewa har yanzu ba a samu gagarumin sauki ba, ana sa ran gidajen mai za su fara rage farashi cikin kwanaki kaɗan da ke tafe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Yayin da farashin ɗanyen mai ke ci gaba da raguwa bayan yarjejeniyar Amurka da Iran, matatar Dangote ta rage farashin fetur ga 'yan kasuwa daga N1,250 zuwa N1,175.

Sai dai gidajen mai ba su rage farashin da masu amfani ke saya ba tukuna, domin har yanzu da yawa suna sayar da fetur a kusan N1,280 kan kowace lita, kamar yadda aka gani a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: Matatar Dangote ta rage farashin man fetur bayan yarjejeniyar Amurka, Iran

Ana sakawa mota fetur
Wani mai mota na shan fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wannan ya sa sauran masu rumbunan ajiya suka rage farashinsu zuwa kusan N1,180, kamar yadda aka wallafa a shafin Petroleumprice.ng

Masu kasuwancin man fetur a Najeriya sun danganta hakan da buƙatar sayar da tsohon kaya domin kauce wa asara kafin rage farashin.

Sabon farashin mai da ake fata

Da yake magana a wata hira, sakataren yaɗa labarai na kungiyar PMAN, Chinedu Ukadike, ya ce ana iya sayar da fetur tsakanin N1,200 zuwa N1,250 a Legas, yayin da a wasu wurare zai iya kasancewa kusan N1,300.

A cewarsa, masu gidajen mai ba su rage farashi ba tukuna saboda da yawa har yanzu suna da tsohon kaya a hannunsu, yana mai kira ga ‘yan Najeriya da su yi haƙuri.

Chinedu Ukadike ya ce mutane kan yi tsammanin a rage farashi nan take, alhali hakan zai jawo asara ga waɗanda suka sayi mai da tsohon farashi.

Bayan rage farashin da Dangote ya yi, Punch ta wallafa cewa Ukadike ya ce:

Kara karanta wannan

Masifa ta fada Amurka, jirgin soji ya fado, jama'a da sojoji sun mutu

“Wannan sanarwar ta ba waɗanda ke da tsohon kaya damar sayar da shi gaba ɗaya, tare da shiri domin karɓar sabon kaya,”
Jama'a na sayen man fetur
Yadda aka yi layin mai a gidan man fetur. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An samu tsaikon jigilar mai

Ukadike ya ƙara da cewa yawanci ana samun tsaiko wajen ɗaukar mai daga matatar Dangote duk lokacin da aka sanar da sabon farashi, domin bai wa masu kasuwanci damar sayar da tsohon kaya.

“Matatar Dangote ta sanar da sabon farashi, ana samun tsaiko sosai wajen ɗaukar mai. Wannan yana ba waɗanda suka sayi sabon kaya damar sayar da tsohon kayan cikin kwana ɗaya ko biyu.
"Sabon kaya ya shiga kasuwa, tsarin samarwa da farashi zai daidaita. Tabbas daga gobe da Juma’a mutane za su fara ganin sabon farashin,”

In ji shi.

An nemi saka tallafin mai

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kungiyar kwadago ta TUC Festus Osifo ya bukaci gwamnatin Najeriya ta sa tallafin man fetur ga 'yan kasa.

Osifi ya bayyana cewa duk da gwamnatin Bola Tinubu ba ta son maido tallafin mai kai tsaye, ya kamata ta sake tunani kan yadda za ta saukakawa al'umma.

Shugaban TUC ya ce akwai hanyar da za a bi wajen hada kai da matatar Dangote wajen rage masa kudin danyen mai domin kudin fetur ya sauka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng