Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Mambobin majalisar wakilai a ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu sun yi watsi da wata bukata na kwaso yan Najeriya da ake zargin sun shiga halin matsi a kasar China biyo bayan barkewar cutar Coronavirus.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da tsarin ba da takardar biza ta Najeriya na shekarar 2020.Ya gabatar da takardar ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu.
Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin tarayya za ta sallami wadanda suka amfana daga shirin tallafinta na N-Power a karshen shekarar nan.
Iyalan marigayi Alhaji Shehu Idris sun koka wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan shirin da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ke yi na rusa wata kadara mallakar mahaifinsu a Gusau, babbar birnin jihar Zamfara.
Kakakin yan sandan birnin tarayya, DSP Anjuguri Manzah a Wani jawabi da ya saki a ranar Litinin, ya ce jami’an rundunar sun kama masu laifin hudu bayan sun amsa wani kira mai cike da damuwa a ranar Lahadi da misalin karfe 5:30.
Rahotanni sun kawo cewa ministan sufuri na kasar, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta kara farashin tikitin jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja ba saboda a ba wa talakawa dama.
Zhou Pingjian, jakadan kasar China a Najeriya, ya ce ofishin jakadancin kasar ta dakatar da ba yan Najeriya biza. Hakan, a cewarsa yana daga cikin kokarin da ake na magance cutar coronavirus da ya billo a kasar Asiya.
Rikicin jihar Edo ta dauki sabon salo yayinda gwamnatin jihar ta nemi a kama tare da hukunta Kwamrad Adams Oshiomhole, kan rashin bin umurninta.
Ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ke Orlu, jahar Imo ta kama da wuta a ranar Litinin, 3 ga watan Fabrairu. Lamarin ya fara ne da misalin karfe 6:00 na asuba.
Aisha Musa
Samu kari