"Ba Ciwon Suga ba ne": Yaron Janar Rabe Ya Fallasa Abin da Ya Yi Zargin Ya Kashe Mahaifinsa

"Ba Ciwon Suga ba ne": Yaron Janar Rabe Ya Fallasa Abin da Ya Yi Zargin Ya Kashe Mahaifinsa

  • Yaron Janar Rabe Abubakar mai ritaya, Isyaka ya ce mahaifinsa ba ya fama da ciwon sukari ko hawan jini
  • Ya ce iyalansu ba su yarda da bayanin gwamnatin Katsina kan musabbabin rasuwar marigayin ba
  • Har yanzu matar marigayin tana hannun masu garkuwa da mutane, sabanin jita-jitar da ake yaɗawa cewa ta dawo gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Ɗaya daga cikin ’ya’yan marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, Isyaka Rabe, ya yi watsi da ikirarin da gwamnatin jihar Katsina a kan ajalin mahaifinsa.

Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga gwamnatin jihar Katsina da ga ce Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya ya mutu ne sakamakon matsalolin ciwon sukari da hawan jini.

Kara karanta wannan

Yaron Janar Rabe ya nemi amsa kan yadda Gwamnati ta karɓo gawar mahaifinsu

Iyalan Janar Rabe Abubakar mai ritaya sun magantu a kan sababin mutuwarsa
Manjo Janar na rundunar sojin Najeriya, Rabe Abubakar mai ritaya Hoto: Mobile Media Crew
Source: Twitter

A wata hira da ya yi da Deutsche Welle Hausa a ranar Lahadi 14 ga watan Yuni, 2026 Isyaka ya bayyana cewa rahotannin da ke danganta rasuwar mahaifinsa da ciwon sukari ba su da inganci.

Janar Rabe ba shi da ciwon suga

Daily Trust ta wallafa cewa Isyaka Rabe, marigayin ba shi da tarihin fama da ciwon sukari ko hawan jini a rayuwarsa, sabanin yadda gwamnati ta yi iƙirari.

Isyaka ya kuma bayyana cewa wasu mutane na ganin wataƙila Janar Rabe ya rasu ne sakamakon cizon maciji, bisa ga abin da suka gani a cikin bidiyon ƙarshe da masu garkuwa da mutanen suka fitar.

Sai dai ya jaddada cewa Allah kaɗai ne Ya san ainihin abin da ya yi sanadin rasuwar mahaifinsa da tuni aka yi wa sutura.

Ya ce:

"Ban yarda cewa ciwon sukari ne ya kashe shi ba. A ganinmu, bugun zuciya ne ya yi ajalinsa. Idan ka duba, an ɗaure ƙafafunsa. Haka kuma wasu sun ce yana tafiya kafin ya rasu. Don haka Allah ne kaɗai Ya san gaskiyar abin da ya faru."

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi martani da Janar Rabe Abubakar ya mutu a hannun 'yan bindiga

Iyalan Janar Rabe sun roki gwamnati

Isyaka ya kuma bayyana cewa mahaifiyarsa, wadda aka sace tare da mahaifinsa, har yanzu tana hannun masu garkuwa da mutane.

Ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an sake ta tare da mika kokensu ga gwamnatin ta ceto ta.

Yaran Janar Rabe sun yi rokon a ceto mahaifiyarsu
Hajiya Amina Abubakar, matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar Hoto: Katsina New Post
Source: Facebook

A cewarsa:

"Duk wanda ya ce an saki mahaifiyata, ni Isyaka Rabe, ɗan Manjo Janar Rabe, ina cewa ƙarya yake yi. Ba a sake ta ba. Har yanzu tana hannunsu."

An sanar da sace Janar Rabe Abubakar da matarsa ne a ranar 30 ga watan Mayu, 2026 a jihar Katsina bayan ya tashi daga Kaduna.

A ranar 6 ga Yuni, 2026, masu garkuwa da mutanen sun nemi a saki ƴan bindiga uku da ake tsare da su tare da mayar masu da dabbobin da suka ce an ƙwace yayin ayyukan tsaro domin su saki ma'auratan.

Iyalan Janar Rabe sun nemi bayanai

A wani labarin, kun ji cewa iyalan marigayi Janar Rabe Abubakar sun nemi bayani kan yadda aka karɓo gawarsa daga hannun ’yan bindigan da suka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Yadda aka birne Janar Rabe da ya rasu a hannun 'yan bindiga cikin jimami a Katsina

Ɗan marigayin, Isyaka Rabe Abubakar, ya ce har yanzu mahaifiyarsa na tsare a hannun masu garkuwa da mutane duk da an iya karɓo gawar mahaifinsu daga hannunsu.

Ya bayyana mahaifinsa a matsayin bawan Allah da ke ƙaunar zaman lafiya, mai don jama'a da kuma halaye na gari, tare da addu'ar Allah SWT Ya yi masa rahama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng