Allah ya yiwa wani tsohon dan majalisa rasuwa jim kadan bayan kammala bikin zagayowar ranar haihuwarsa
- Allah ya yiwa sohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Ogun, Hon. Yinka Mafe rasuwa
- Marigayin ya mutu ne a daren ranar Talata, jim kadan bayan bikin cikarsa shekara 46
- Mafe ya yi korafin ciwon kirji bayan bikin inda ya mutu daga bisani
Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Ogun, Hon. Yinka Mafe, ya mutu.
An tattaro cewa ya mutu ne a daren ranar Talata, jim kadan bayan bikin cikarsa shekara 46.
Mafe ya yi korafin ciwon kirji bayan bikin inda ya mutu daga bisani.
An ajiye gawarsa a wajen ajiye gawa na asibitin koyarwa na jami’ar Olabisi Onabanjo (OOUTH).
Asiwaju Yinka Mafe wanda aka haifa a ranar 4 ga watan Fabrairu, 1974, ya yi kansilan unguwa uku a karamar hukumar Sagamu a Disamba 1998, wa’adin da ya kare a 2002.
Ya wakilci mazabar mazabar Sagamu a majalisr dokokin jiha tsakanin 2011 da 2019 a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wacce ta kasance Action Congress of Nigeria (ACN) a baya.
A farkon ranar Talata, Mafe ya shirya taron addu’a a gidansa da ke Emuren don bikin zagayowar ranar haihuwarsa.
KU KARANTA KUMA: Kurunkus: Nathaniel Samuel ya fadi sunan wacce ta tura shi cikin coci da bam (Bidiyo)
An tattaro cewa ya ziyarci fursunoni a cibiyar gyaran halayya, Sagamu kafin bikin zagayowar ranar wanda aka yi a Tenth Planet and Suite a Sagamu wanda ya damu halartan mutane da dama.
A wani labari na daban, mun ji cewa hukumar kashe gobara ta jahar Zamfara ta sanar tare da tabbatar da tashin gobara a gidan wani dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe, Alhaji Kabiru Mai Palace, dake garin Gusau a ranar Talata.
Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito mataimakin darakta a hukumar, Abdullahi Jibo ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da wakilinta, inda yace wutar ta tashi ne a gidan dake unguwar Yarima, cikin garin Gusau.
Malam Jibo yace alamu sun nuna wutar lantarki ne ya yi sanadiyyar tashin gobarar, saboda a cewarsa da misalin karfe 10:30 na safiyar talata suka samu kiranye daga unguwar game da tashin gobarar, inda yace ba tare da bata lokaci ba jami’ansu suka isa gidan, suka kuma kashe wutar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng