"Suna Tare cikin Daki"; Tsohon Jami'in DSS Ya Fadi Abin da Ya Kashe Janar Sani Abacha

"Suna Tare cikin Daki"; Tsohon Jami'in DSS Ya Fadi Abin da Ya Kashe Janar Sani Abacha

  • Shekaru 28 bayan rasuwarsa, har yanzu ana ba da mabanbantan bayanai kan abin da ya kashe marigayi Janar Sani Abacha
  • Tsohon darakta a hukumar tsaron farin kaya (DSS), Dennis Amachree, ya warware zare da abawa kan abubuwan da suka faru
  • Amachree ya bayyana cewa ya yi tambayoyi ga shaidar da take ganau ba jiyau baokacin marigayi tsohon shugaban kasar ya rasu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin darakta na hukumar tsaron farin kaya (DSS), Dennis Amachree, ya yi magana kan mutuwar marigayi Janar Sani Abacha.

Dennis Amachree ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar na mulkin soja, ya rasu ne sakamakon bugun zuciya.

An sake yin maganar mutuwar Janar Abacha
Marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Sani Abacha Hoto: Issouf Sanogo
Source: Getty Images

Amachree ya bayyana hakan ne a cikin sabon littafinsa da aka fito da shi, wanda ya yi magana a kansa a lokacin wata hira da ya yi da tashar TVC News.

Kara karanta wannan

Mele Kyari: Kwamitin majalisa ya umarci cafke tsohon shugaban NNPCL kan badakalar N210trn

Abin da aka ce kan mutuwar Sani Abacha

Tsohon mataimakin daraktan na DSS ya ba da labari daki-daki na binciken da aka gudanar bayan mutuwar Abacha a ranar 8 ga watan Yuni, 1998.

Yayin da yake magana a lokacin hirar, Amachree ya yi watsi da wasu ra'ayoyi da aka daɗe ana kawo wa game da mutuwar Abacha, inda ya jaddada cewa da yawa daga cikin waɗanda suka yi magana kan lamarin ba su da masaniya kan ainihin abubuwan da suka auku.

“Mutane da yawa sun fito da labarai mabanbanta game da abin da ya faru, amma ba su da masaniya kan gaskiyar lamarin. Suna kallon abubuwan ne daga waje sannan su yanke hukunci.”
“Wasu ma sun yi iƙirarin cewa wasu abubuwa ne suka haddasa mutuwarsa, amma su ba likitoci ba ne kuma ba za su iya faɗa da tabbaci abin da ya kashe shi ba."

- Dennis Amachree

Jami'in DSS ya yi tambayoyi ga ganau

Amachree ya bayyana cewa babbar ganau ba jiyau ba kan lamarin wata mace ce da take tare da Abacha jim kaɗan kafin mutuwarsa. A cewarsa, ta isa gidan ne tare da yayarta, wadda aka ce Abacha ya santa.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: An hallaka mawaki dan asalin Najeriya a Burtaniya

“Yarinyar da ke tare da shi lokacin da ya mutu daga baya aka kawo mani ita domin yi mata tambayoyi. Lokacim da ta shigo ofishina, abu na farko da ta ce shi ne, ‘Ba ni na kashe shi ba.’ Ta fito fili ta faɗi hakan kai tsaye."

- Dennis Amachree

Me shaidar ta fada?

Ya bayyana cewa bayan ya yi hira da ita, bai samu wani dalili na shakkar labarin da ta ba da na yadda abubuwan suka auku ba.

“Dole ne na yi amanna da ita saboda ba ta da dalilin yi mini ƙarya. Ban samar da wani yanayi da zai sa ta ji tsoro ko barazana ba.”
“Labarinta shi ne kaɗai sahihin bayani na shaidar da ya gani da idonsa game da abin da ya faru, saboda babu wani mutum daban da ke cikin ɗakin tare da su."

- Dennis Amachree

An yi magana kan mutuwar Janar Abacha
Tsohon shugaban kasa, marigayi Janar Sani Abacha Hoto: AFP
Source: Getty Images

Abin da ya kashe Janar Abacha

Bisa ga shaidar da ya karɓa da kuma binciken da ya biyo baya, Amachree ya ce ya yi amanna Abacha ya mutu ne sanadiyyar lokacinsa ya yi.

“Daga dukkan abin da ta shaida mini da kuma abin da na tattara a lokacin bincike, na yi imani mai ƙarfi cewa bugun zuciya ne."

Kara karanta wannan

Shugaba a majalisa ya faɗi lokacin da za a amince da dokar ƴan sandan jihohi

"Ba ta san ya mutu ba lokacin da take tare da shi, amma daga baya ta fahimci akwai abin da ba daidai ba. A bisa bincikena, mutuwarsa ta kasance ne sakamakon bugun zuciya."

- Dennis Amachree

Obasanjo ya magantu kan Abacha

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda marigayi Janar Sani Abacha, ya yi kokarin kashe shi.

Obasanjo ya bayyana cewa bayan kama shi tare da Janar Shehu Musa Yar’Adua da dan kasuwa, Chief MKO Abiola, Abacha ya kitsa wani makirci na kawar da su daga doron kasa.

Tsohon shugaban kasar ya ce Abacha ya sha alwashin cewa su ukun ba za su fita daga gidan yari da rai ba, domin ya samu damar ci gaba da mulki har abada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng