Da dumi-dumi: Buhari ya gabatar da tsarin ba da bizar Najeriya na 2020

Da dumi-dumi: Buhari ya gabatar da tsarin ba da bizar Najeriya na 2020

- Shugaba Buhari ya gabatar da tsarin ba da takardar biza ta Najeriya na shekarar 2020

- Ya gabatar da takardar ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu

- Yan Afrika da ke da fasfot kuma suke muradin shigowa kasar don ziyarar kasuwanci ko bude ido za su ci moriyar sabon tsarin sosai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da tsarin ba da takardar biza ta Najeriya na shekarar 2020.

Ya gabatar da takardar ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu. Takardar ya kasance wanda aka sake bi ne.

Mai taimaka wa shugaban kasar kan kafafen sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Shugaba Buhari ya ce an sake duba tsarin bayar da bizan ne don janyo sabbin dabaru na musamman da ilimi daga kasashen waje.

An fito da tsarin bizar 2020 ne don habbaka kasuwanci da cimma manufar hada kan Afrika ta bizar da zarar an iso ga wadanda ke rike da fasfot din kungiyar kasashen Afrika.

KU KARANTA KUMA: Fada da cikawa: Gwamnatin jihar Kaduna na bi titi-titi domin damke yaran da basu zuwa makaranta

Yan Afrika da ke da fasfot kuma suke muradin shigowa kasar don ziyarar kasuwanci ko bude ido za su ci moriyar sabon tsarin sosai, inda za a basu damar tsayawa a kasar har tsawon kwanaki 90.

A wani labari na daban, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika takardar neman karin bayani ga ministan aikin noma, Sabo Nanono, a kan amincewa wasu kamfanoni da yayi kan su shigo da takin gona. Hakan kuwa ya ci karo da umarnin shugaban kasa Buhari na sarrafa taki a cikin gida Najeriya.

Jaridar ThisDay ta gano cewa ministan ya ba wasu masu shigo da taki lasisin ne don a hadiye gibin rashin takin da ake fama da shi a kasar nan.

An gano cewa abinda ministan yayi, yayi karantsaye ga dokar da shugaban kasa ya bada a shekaru uku da suka gabata don tabbatar da ana samar da taki a gida Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel