Kada ka bari Matawalle ya ci mutuncinmu - Iyalan Shehu Idris ga Buhari

Kada ka bari Matawalle ya ci mutuncinmu - Iyalan Shehu Idris ga Buhari

Iyalan marigayi Alhaji Shehu Idris sun koka wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan shirin da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ke yi na rusa wata kadara mallakar mahaifinsu a Gusau, babbar birnin jihar Zamfara.

A wani korafi da suka aike ma Shugaban kasar, dauke da sa hannun ahlin da suka hada da Aminu Shehu Idris, Salisu Shehu Idris da kuma Rabiu Shehu Idris; sun zargi gwamnan da cin mutuncin ahlin.

Idan za a tuna, Alhaji Mukhtar Shehu Idris, Koguna Gusau, wanda daya daga cikin ahlin ne ya kasance zababben gwamnan Zamfara kafin kotun koli ta soke nasararsa yan kwanaki bayan rantsar dashi a shekarar bara.

Kada ka bari Matawalle ya ci mutuncinmu - Iyalan Shehu Idris ga Buhari
Kada ka bari Matawalle ya ci mutuncinmu - Iyalan Shehu Idris ga Buhari
Asali: UGC

Wasikar ya zo kamar haka: “Ya mai girma, muna son janyo hankalinka zuwa ga wani lamari mai sanya damuwa da ahlinmu suka tsinci kansu a karkashin gwamnatin Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.

“A shekarar bara, wani suna da ba a sani ba wanda aka yi zargin daya daga cikin ahlinmu ne ya bayyana a badakalar ma’aikatan bogi a kokari na bata mana suna wanda muka yi watsi dashi tare da neman ban hakuri.

Sannan a yanzu gwamnatin jihar Zamfara ta sanya alamar rushe gidan ahlinmu da wani masallaci da mahaifinmu ya gina sama da shekaru 40.

“An tursasamu amfani da wannan damar domin kawo kukanmu saboda muna ganin hakan a matsayin mai matukar hatsari cin mutuncin mutane a siyasance da gwamnoni suka dauki hanyar yi.

“Mun fadi hakan ne saboda lamari makamancin haka da ya faru da iyalan marigayi Alhaji Olusola Saraki a jihar Kwara. Zababben gwamna a 2019 a jihar Zamfara, Alhaji Mukhtar Shehu Idris (Kogunan Gusau) karkashin jam’iyyar , wanda kotun koli ta soke nasararsa ya kasance ahlin gidanmu mai albarka.

“Yallabai, mun kasance ahli masu bin doka kuma cikin iyayen jihar Zamfara. Mahaifinmu ya jajirce don cigaban jihar amma a yanzu ake hukunta shi don ya haifi da dake jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wacce ta banbanta da ta Gwamna Matawalle na PDP.

KU KAANTA KUMA: Yan sanda sun cafke manyan masu garkuwa da mutane su 4 a hanyar Abuja-Lokoja

“Ya mai girma a madadin ahlimu da dukkanin yan Najeriya da hakkinsu ya rataya a wuyanka a matsayin shugabannin dukkanin al’umma, mun zo gare ka domin shawarci dukkanin gwamnoni a kasa da su yi adalci ga al’umma ba tare da la’akari da banbancin akida ba kamar yadda kake nunawa a duk lokacin da kake mu’amala da su."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel