Za a sallami yan N-Power kafin karshen shekarar nan – Gwamnatin tarayya
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a salami wadanda suka amfana da shirin N-Power kafin karshen shekarar 2020
- Ministar harkokin agaji, hana yaduwar annoba da ci gaban jama’a, Sadiya Farouq ce ta bayyana hakan a lokacin wata hira da manema labarai
- Farouq ta ce ya kamata ace rukunin farko na shirin ya kare a tun 2018
Sai dai idan wani ikon Allah, amma dai za a sallami wadanda suka amfana daga shirin tallafi na gwamnatin tarayya wato N-Power a karshen shekarar nan.
Legit.ng ta rahoto cewa ministar harkokin agaji, kula da annoba da cigaban jama’a, Sadiya Umar Farouq, ce ta bayyana a wani bidiyo da jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamnatin tarayya za ta kawo karshen shirin kafin karshen shekarar.
Ministar ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ce a farkon kafa shirin an tsara cewa za ta gudana ne na tsawon shekaru biyu, inda ta kara da cewa dukkanin wadanda suka amfana na sane da cewar ba za a bukaci aikinsu ba bayan shekaru biyu.
Ta kara da cewa an kafa shirin ne domin tallafawa matasa marasa aikin yi, musamman wadanda suka kammala karatu, cewa ya kamata a ce rukunin farko na shirin ya kare a 2018.
Farouq ta kuma bayyana cewa masu hikima cikin wadanda suka amfana daga shirin sun rigada sun tara daga cikin kudin da ake basu duk wata domin makomarsu a nan gaba.
KU KARANTA KUMA: Kada ka bari Matawalle ya ci mutuncinmu - Iyalan Shehu Idris ga Buhari
Ministar ta kara da cewa ma’aikatarta da sauran manyan masu fada a ji za su kawo hanya mafi dacewa don ganin yadda wadanda suka amfana za su samu wani abun dogaro bayan an sallame su.
A wani labari na daban, mun ji cewa bayan barazanar da gwamnatin jihar Kaduna ta yiwa iyayen da suke hana yaransu zuwa makarantun Boko duk da cewa gwamnatin ta mayar kyauta, an fara daukan yaran da aka gani a titi lokacin makaranta.
Hotuna da suka yadu a shafukan Soshiyal Midiya sun nuna jami'an wata sabuwar hukumar a jihar Kaduna da sunan 'Edumarshal' a kan titi daga cikin titunan jihar da yara cikin mota.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng