Trump zai Ajiye Nuna Isa Ya ba Iran Dala Biliyan 24 saboda Yarjejeniya
- An fara samun cikakkun bayanai game da abubuwan da ke cikin kundin da Amurka da Iran suka amince da shi kafin amincewa da yarjejeniya
- Wani rahoto ya nuna cewa daga cikin muhimman abubuwan da aka amince da su shi ne mika biliyoyin daloli da Amurka za ta yi ga Iran
- Ana ce Amurka za ta saki dala biliyan 12 daga cikin kadarorin Iran da aka kakaba wa takunkumi kafin a fara tattaunawar da za ta biyo baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Wasu rahotanni da suka fito daga gwamnatin Tehran sun nuna cewa Amurka za ta saki dala biliyan 12 na kadarorin Iran da aka rike.
Takardar da wata tasha a Iran ta fitar ta ambaci sakin dala biliyan 24 na kadarorin Tehran da aka sakawa takunkumi a lokacin tattaunawar kwanaki 60 da za ta fara bayan kammala fahimtar juna.

Source: Getty Images
Al Jazeera ta wallafa cewa Iran ta kafa sharadin cewa dole rabin kuɗin ya shiga asusunta kafin fara tattaunawar da za ta yi da kasar Amurka.
Me yarjejeniyar ta ƙunsa?
A cewar wani rahoto da ake jingina shi da kamfanin dillancin labarai na Mehr da ke kasar Iran, daftarin yarjejeniyar ya ƙunshi mataki ko abubuwa 14.
Abubuwan da ke cikin yarjejeniyar sun haɗa da dakatar da yaƙi nan take kuma har abada a dukkan fage-fage, ciki har da Lebanon.
Haka zalika akwai ɗage katangar jiragen ruwa cikin kwanaki 30; alƙawarin Amurka na janye dakarunta daga yankunan da ke kusa da Iran; da kuma sake buɗe mashigar Hormuz.
Daftarin ya kuma ambaci dakatar da takunkumin sayar da mai, cimma yarjejeniya ta ƙarshe kan batun nukiliya cikin kwanaki 60 bayan sanya hannu kan yarjejeniyar.
A karshe an ambaci sakin dala biliyan 24 na kadarorin Iran da aka daskarar a lokacin tattaunawar kwanaki 60 da za a fara a nan gaba.

Source: Getty Images
An ce Iran ta ce ba za a fara tattaunawar ƙarshe ba har sai an saki rabin kadarorin Iran da aka daskarar tare da ɗage takunkuman da suka shafi mashigin ruwa na Hormuz.
Ta ƙara da cewa an cire batutuwan da suka shafi shirin makamai masu linzami na Iran da kuma goyon bayanta ga ƙungiyoyin gwagwarmaya daga ajandar tattaunawar.
Me Iran da Amurka suka ce?
Sakatariyar kwamitin tsaron kasa ta Iran ta ce za a gudanar da sanya hannu kan takardar fahimtar juna a hukumance a ranar Juma’a, 19 ga Yunin 2026.
Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya ce tsagaita wutar da aka sanar na iya buɗe sabon babin rayuwa a Gabas ta Tsakiya.
Anadolu ta rahoto ya danganta cimma yarjejeniyar da diflomasiyyar Trump tare da ƙasashen yankin Tekun Fasha da sauran abokan hulɗa na yankin.
Za a cirewa Iran takunkumi
A wani labarin, kun ji cewa kasar Iran ta fara samun alheri daga kasashen Turai bayan cimma yarjejeniya da Amurka a ranar Lahadi.
Birtaniya, Faransa, Italy da Jamus da suke karkashin E4 sun amince za su cire wa Iran takunkumi idan aka kammala amincewa da yarjejeniyar.
Janye takunkumin zai ba Iran damar cigaba da hulda tare da kasashe da dama musamman na Turai ba tare da wata tangarda ba.
Asali: Legit.ng


