Amurka ta maido wa Najeriya N112b da Gwamna Bagudu ya taimaka wajen wawurewa

Amurka ta maido wa Najeriya N112b da Gwamna Bagudu ya taimaka wajen wawurewa

Gwamnatin kasar Amurka ta mayar wa Najeriya da naira biliyan da tsohon shugaban kasa a mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha ya wawure.

Gwamnatin Birtaniya ce ta kwace kudin da aka boye a tsibirin Jersey bayan shari'ar da aka yi ta yi kan batun - ciki har da kalubalantar Amurka a shekarar 2014.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ne aka baiwa kudin a wancan lokacin ya loda, sannan ya yi jigilar fitar da su kasar Amurka da Jersey.

Kafin ya zama Gwamnan Jihar Kebbi, Bagudu ya yi sharafi a zamanin mulkin Abacha, inda ya taka gagarumar rawa wajen lodi, jigila da kuma karakainar kimshe kudade da aka karkatar da su a madadin Abacha, shaugaban mulkin soja wanda ya rasu cikin 1998.

Wadannan makudan kudaden da aka dawo wa Najeriya dai an tabbatar da cewa su ne mafi yawa da Tsibirin Jersey ya taba maida wa kasar da aka sato kudin a tarihi.

Wadannan makudan kudaden da za a maido wa Najeriya har naira bilyan 112, baya cikin lissafin wasu naira bilyan 59.3 wadanda Bagudu ya amince zai maido wa Najeriya tun a cikin 2003.

An tattaro cewa Atiku Bagudu ya amince zai maida kudin Najeriya cikin 2003, a bisa yarjejeniyar cewa Tsibirin Jersey ta rufa asiri a janye sammacin da kasar ta tura Amurka, inda kasar ta Jersey ta nemi Amurka ta kama mata Bagudu ta mika shi domin ya fuskanci hukuncin laifin harkalla a can kasar ta Jersey.

Rahoton ya kuma bayyana cewa jami’an tsaron kasar Amurka sun taba tsare Gwamna Bagudu a kurkuku, tsawon watanni shida. An tsare shi ne saboda rawar da ya taka wajen yi wa tsohon shugaban Mulkin Soja, Janar Sani Abacha aikin fito da dillancin fitar da kudaden sata daga Najeriya zuwa kasashen waje.

An kiyasta cewa Abacha ya saci akalla dalar Amurka biliyan 2.2 daga arzikin Najeriya a lokacin da ya ke mulki. Ya rasu cikin 1998.

An tattaro cewa Bagudu ya rika yin wannan harkalla tare da wasu ‘yan uwan sa ko iyalan sa, wasu jami’an gwamnati na lokacin Abacha da kuma dan Abacha, Mohammed.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Buhari ya gabatar da tsarin ba da bizar Najeriya na 2020

Har ila yau rahoton ya nuna cewa sun yi ta amfani da sunayen wasu kamfanoni na bogi, suna karkatar milyoyin daloli zuwa kasashen ketare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel