Dalilin da ya sa ba za mu kara farashin tikitin jirgin kasa ba – Amaechi

Dalilin da ya sa ba za mu kara farashin tikitin jirgin kasa ba – Amaechi

Rahotanni sun kawo cewa ministan sufuri na kasar, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta kara farashin tikitin jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja ba saboda a ba wa talakawa dama.

Ameachi wanda ya bayyana a shirin Channels TV na Sunrise Daily ranar Litinin, ya ce yana ankare da irin kiraye-kirayen da ake yi na kara farashin domin ma'aikatarsa ta samu kudin biyan bashin da ta ciyo na ayyukan da ta yi da kuma yin tattalin jirgin.

Sai dai Amaechi ya ce akasari jiragen kasa ba su fiya samun riba ba daga farashin tikiti a fadin duniya domin ana samar da su ne saboda samun sauki.

Dalilin da ya sa ba za mu kara farashin tikitin jirgin kasa ba – Amaechi
Dalilin da ya sa ba za mu kara farashin tikitin jirgin kasa ba – Amaechi
Asali: UGC

Channels Ta ta rawaito inda ya ke cewa: "Idan muka kara farashin tikitin ya za mu yi da talakawa masu son zuwa Kaduna daga Abuja? Ya batun talakan da ke aiki a Abuja kuma yake zaune a Kaduna domin ya saukaka wa kansa rayuwa?

KU KARANTA KUMA: Abinda Buhari ya fada wa Lawan da Gbajabiamila a kan tsaro yayin ganawarsu

“Saboda haka, a duniya baki daya ana saukaka farashin jirgi saboda talaka ya samu hanyar zirga-zirga cikin sauki. Ana samar da shi ne domin ya habbaka tattalin arzikin kasa.

"Tattalin arzikin kasar zai cike gurbin. Duba yawan harkokin da kake kokarin ginawa ta wannan hanya, yawan kamfanonin da ka kirkira, sai kuma ka duba yawan harajin da suke biyanka."

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa kasa da mako guda bayan gwamnatin kasar Amurka ta sanya haramcin bayar da biza kan Najeriya da wasu kasashen Afrika, Zhou Pingjian, jakadan kasar China a Najeriya, ya ce ofishin jakadancin kasar ta dakatar da ba yan Najeriya biza.

Hakan, a cewarsa yana daga cikin kokarin da ake na magance cutar coronavirus da ya billo a kasar Asiya.

Legit.ng ta rahoto cewa sama da mutane dari uku ne suka mutu a kan mummunar annobar a China, yayinda kungiyar lafiya ta duniya ta kaddamar da shi a matsayin matsalar duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel