Yanzu Yanzu: Ofishin jakadancin China ta dakatar da ba yan Najeriya biza

Yanzu Yanzu: Ofishin jakadancin China ta dakatar da ba yan Najeriya biza

- Zhou Pingjian, jakadan kasar China a Najeriya, ya ce ofishin jakadancin kasar ta dakatar da ba yan Najeriya biza

- Ya ce hakan yana daga cikin kokarin da ake na magance cutar coronavirus da ya billo a kasar Asiya

- Sama da mutane dari uku ne suka mutu a kan mummunar annobar a China, yayinda kungiyar lafiya ta duniya ta kaddamar da shi a matsayin matsalar duniya

Kasa da mako guda bayan gwamnatin kasar Amurka ta sanya haramcin bayar da biza kan Najeriya da wasu kasashen Afrika, Zhou Pingjian, jakadan kasar China a Najeriya, ya ce ofishin jakadancin kasar ta dakatar da ba yan Najeriya biza.

Hakan, a cewarsa yana daga cikin kokarin da ake na magance cutar coronavirus da ya billo a kasar Asiya, jaridar The Nation ta ruwaito.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa sama da mutane dari uku ne suka mutu a kan mummunar annobar a China, yayinda kungiyar lafiya ta duniya ta kaddamar da shi a matsayin matsalar duniya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa maimata irin abinda akayi lokacin cutar SARS a 2003, gwamnatin jihar Wuhan a kasar Sin ta kaddamar da ginin asibitoci biyu Leishenshan da Huoshenshan a ranar 23 ga watan Junairu, 2020.

Cikin kwanaki 10, gwamnatin ta kammala ginin katafaren asibiti mai gado 1000 domin yakan cutar Coronavirus da ya bulla a garin Wuhan kuma ya yadi a akalla kasashen duniya 25 yanzu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin Edo ta bukaci kama Oshiomhole tare da hukunta shi cikin gaggawa

A ranar Lahadi, 2 ga Febrairu, an kammala ginin asibitin Huoshenshan kuma zau Litinin, 3 ga Febrairu, 2020. Farawa da iyawa, an tura likitocin 1,400 daga hukumar Soji domin jinyar marasa lafiya a Asibitin.

Ku sani cewa Coronovirus ta na cikin dangin cututtuka irin su MERS da SARS da ke kawo matsalar numfashi. Cutar ta saba addabar dabbobi kafin yanzu ta bayyana jikin mutum.

Yanzu wannan cuta ta yi kamari ne a Sin. Bayan nan ta fara shiga kasashe kamar Thailand, Koriya ta Kudu, Taiwan, Jafan da Amurka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel