Amaechi: Jam'iyyar ADC Ta Sanar da Abokin Takarar Atiku a Zaben 2027

Amaechi: Jam'iyyar ADC Ta Sanar da Abokin Takarar Atiku a Zaben 2027

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya samu abokin takara domin fafatawa a zaben shekarar 2027
  • Jam'iyyar ADC ta sanar da cewa ta zabi tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin dan takararta na mataimakin shugaban kasa a zaben 2027
  • ADC ta bayyana Amaechi a matsayin mutum mai gogewa duba da irin manyan mukaman da ya taba rikewa a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam'iyyar ADC ta sanar da abokin takarar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 da ake tunkara.

ADC ta zaɓi tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar domin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Amaechi ya zama abokin takarar Atiku a zaben 2027
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi Hoto: @atiku, @ChibuikeAmaechi
Source: Twitter

Sakataren yada labarai na ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Yadda Amaechi yake fuskantar matsin lamba kan zama abokin takarar Atiku a ADC

Meyasa ADC ta zabi Amaechi?

Jam'iyyar ta ce zabar Amaechi ya biyo bayan shawarwarin da aka yi, kuma hakan ya nuna bajintarsa na kasancewa wanda ya zo na biyu a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na ADC.

Bolaji Abdullahi, ya siffanta tikitin na Atiku da Amaechi a matsayin “tikitin haɗin kai da ceto” wanda ke da ikon magance ƙalubalen Najeriya.

“Haɗin gwiwar da aka tsara tsakanin mai girma Atiku Abubakar da Rt. Hon. Rotimi Amaechi ya wuce kawai kawance na siyasa, haɗuwar wasu fitattun 'yan kishin ƙasa ne guda biyu masu gogewa."
"Sanannu a kowane sashe na ƙasa, da kuma juriya na shugabanci da ake buƙata domin ceto Najeriya daga ƙalubalenta na yanzu da kuma mayar da ƙasar ga wani sabon zamani na wadata, tsaro, da ci gaba wanda ya haɗa kowa da kowa."

- Bolaji Abdullahi

ADC ta ce Amaechi na da gogewa

A cewar jam'iyyar, gogewar siyasa da ta gudanarwa ta Amaechi ta sa ya dace sosai da wannan matsayi, duba da cewa ya taɓa yin aiki a matsayin shugaban majalisar dokoki ta jihar Rivers, gwamnan jihar Rivers na wa'adi biyu, da kuma Ministan sufuri.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani kan rasuwar Manjo Janar Rabe a hannun 'yan bindiga

“Kaɗan ne daga cikin shugabannin siyasa a Najeriya a yau suke da irin wannan gogewa a tsakanin sassan majalisar dokoki da na zartarwa na gwamnati."
"Wannan zurfin gogewa zai kasance mai matuƙar amfani wajen tallafa wa gwamnati ta gaba ta ADC tun daga rana ta farko."

- Bolaji Abdullahi

Amaechi ya zama abokin takarar Atiku a zaben 2027
Atiku Abubakar tare da Rotimi Amaechi Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Amaechi na da tasiri a Kudancin Najeriya

Jam'iyyar ADC ta kuma ce tasirin Amaechi a shiyyar Kudu-maso-Kudu da kuma fadin Kudancin Najeriya zai ƙarfafa tikitin sannan ya haɓaka karɓuwarsa a matakin ƙasa.

ADC ta yi kira ga mambobin jam'iyyar, abokan kawance, ƙungiyoyin fararen hula, ƙungiyoyin matasa da na mata, da sauran 'yan Najeriya da su tallafa wa yakin neman zaɓenta yayin da ake fara shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Amaechi na fuskantar matsin lamba

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, na fuskantar matsin lamba domin zama abokin takarar Atiku Abubakar a zaben 2027.

Manyan masu ruwa da tsaki sun amince cewa haɗa Atiku da Amaechi shi ne mafi dacewa da muradin ADC a zaben shugaban kasa na 2027 da ake tunkara.

Ana ci gaba da tuntubar Amaechi don ya amince da hakan saboda tasirinsa a siyasar Kudu maso Kudu da kuma gogewarsa a matakin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng