Rahoto: Dalilin da Ya Sa Atiku Ya 'Zabi' Amaechi a Matsayin Abokin Takararsa a 2027

Rahoto: Dalilin da Ya Sa Atiku Ya 'Zabi' Amaechi a Matsayin Abokin Takararsa a 2027

  • Rahotanni sun ce Atiku Abubakar ya amince da Rotimi Amaechi a matsayin abokin takararsa a jam’iyyar ADC kafin zaben 2027
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ADC ta zabi Amaechi saboda tasirinsa a siyasar Kudu maso Kudu da gogewarsa a gwamnatin tarayya
  • Jam’iyyar ADC ta ce tana kokarin ganin cewa ta kauce wa rikicin cikin gida, irin wanda ya dabaibaye PDP dab da babban zaben 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Rahotanni sun ce Atiku Abubakar ya zabi tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 karkashin jam’iyyar ADC.

Majiyoyi masu kusanci da jam’iyyar sun bayyana cewa an dauki matakin ne bayan gudanar da nazari kan yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma domin zakulo wanda zai dace da tikitin.

Kara karanta wannan

1959 zuwa 2026: Lokuta 5 da Hausawa da Ibo suka haɗu a siyasance kafin tafiyar OK a NDC

Majiyoyi sun bayyana dalilin da ya sanya Atiku Abubakar ya zabi Rotimi Amaechi a matsayin abokin takararsa.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da tsohon minista Rotimi Amaechi. Hoto: @atiku, @ChibuikeAmaechi
Source: Twitter

Dalilin Atiku na zabar Amaechi a ADC

A cewar majiyoyin, shugabannin jam’iyyar sun fahimci cewa zaben dan takara daga yankin Kudu maso Gabas ba zai kara musu wata babbar fa’ida ba, la'akari ma da cewa Peter Obi na takara a wata jam'iyyar daban, a cewar rahoton jaridar Tribune.

Rahoton ya nuna cewa da farko an yi tunanin dauko wani gwamna daga yankin Kudu maso Yamma domin cike gurbin mataimakin shugaban kasa.

Sai dai daga baya shugabannin ADC suka yanke hukuncin cewa mutane daga yankin ba za su yarda a musanya masu kujerar shugaban kasa da ta mataimakin shugaban kasa ba.

Hakan ne ya sa aka karkata hankali zuwa yankin Kudu maso Kudu, inda aka ce Amaechi ke da karfi da tasiri saboda gogewarsa a siyasa.

Majiyoyin jam’iyyar sun bayyana cewa tsohon gwamnan na Rivers ya gina manyan alaka tun lokacin da ya yi gwamna da kuma lokacin da ya rike mukamin ministan sufuri a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

ADC: Rahoto ya nuna mutumin da Atiku zai dauka mataimaki a zaben 2027

A cewarsu, wadannan alaka na iya taimaka wa tikitin ADC wajen samun kuri’u a yankuna daban-daban na kasar nan.

ADC na son kauce wa kura-kuran PDP

Wata majiya daga cikin shugabannin jam’iyyar ta bayyana cewa ADC ta kuduri aniyar hada kan dukkan mambobinta domin kauce wa rikicin cikin gida.

Majiyar ta ce shugabannin jam’iyyar ba sa son maimaita kura-kuran da suka haddasa rabuwar kai a cikin PDP kafin zaben shekarar 2023.

“Shugabanninmu sun cimma matsaya cewa kowa zai kasance cikin tafiyar jam’iyyar domin kauce wa korafe-korafen da suka faru a baya,” in ji majiyar.

An jinkirta bayyana Amaechi a hukumance

Rahotanni sun kara da cewa Atiku ya shirya bayyana Amaechi a hukumance tun da farko, amma tafiyar da ya yi zuwa kasashen waje ta sa aka dakatar da sanarwar na wani lokaci.

Wata majiya ta ce da zarar Atiku ya dawo Najeriya, za a gabatar da Amaechi ga jama’a a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na ADC.

A cewar majiyoyin, jam’iyyar na ganin zaben Amaechi wata dabara ce da za ta taimaka wajen jawo kuri’u daga yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta yi magana game da ƙorafin Kwankwaso da barazanar zai bar NDC

Majiyoyi sun ce jam'iyyar ADC ta zabi Rotimi Amaechi domin kauce wa rigingimun da PDP ta shiga a 2023
Jiga-jigan Adawa, ciki har da Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi, David Mark a wajen kaddamar da ADC. Hoto: @atiku
Source: Facebook

Amaechi ya amince da tayin Atiku

Jaridar PM News ta rahoto cewa tsohon shugaban jam'iyyar ADC na jihar Rivers, Leader Sampson ya bada tabbacin cewa Amaechi ya amince ya zama abokin takarar Atiku.

Da 'yan jarida suka tambaye shi ko Amaechi ya karbi tayin, Sampson ya amsa masu da "Eh."

ADC ba ta tabbatar da zaben ba

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, ADC ba ta tabbatar da rahotannin da ke cewa an zabi Rotimi Amaechi a matsayin mataimakin Atiku Abubakar ba.

Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa ba shi da bayanin da zai tabbatar ko karyata batun zaben AmaechiY

Rahotanni sun ce tikitin Atiku da Amaechi zai iya karfafa ADC a Kudu maso Kudu kafin babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com