Coronavirus: 'Gara su zauna a can' - 'Yan majalisa sun yi watsi da bukatar a kwaso 'yan Najeriya daga China

Coronavirus: 'Gara su zauna a can' - 'Yan majalisa sun yi watsi da bukatar a kwaso 'yan Najeriya daga China

- 'Yan majalisar wakilai sun yi watsi da bukatar a kwaso 'yan Najeriya daga China

- Sun ce gara a bar su a can kasar domin a cewarsu China ta fi Najeriya kayayyakin magance lamarin annoar coronavirus da ya shigo

- Duk da kokarin da kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ya yi don shawo kan yan majalisar da kuma bari Mista Okezie ya gabatar da kudirinsa kan lamarin, yan majalisar sun ki bashi damar yin hakan

Mambobin majalisar wakilai a ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu sun yi watsi da wata bukata na kwaso yan Najeriya da ake zargin sun shiga halin matsi a kasar China biyo bayan barkewar cutar Coronavirus.

A cewar yan majalisar wadanda suka yi adawa da bukatar da kakakin majalisar, Benjamin Okezie ya gabatar, kasar China na da ingantattun kayayyakin magance lamarin fiye da Najeriya.

Duk da kokarin da kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ya yi don shawo kan yan majalisar da kuma bari Mista Okezie ya gabatar da kudirinsa yan majalisar sun ki bashi damar yin hakan.

Coronavirus: 'Gara su zauna a can' - 'Yan majalisa sun yi watsi da bukatar a kwaso 'yan Najeriya daga China
Coronavirus: 'Gara su zauna a can' - 'Yan majalisa sun yi watsi da bukatar a kwaso 'yan Najeriya daga China
Asali: UGC

An sha dirama lokacin da wasu da suka gabatar da kudirin su biyu wadanda ya kamata ace sun mara masa baya, suka janye inda suka ki marawa kudirin baya.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Buhari ya gabatar da tsarin ba da bizar Najeriya na 2020

A halin da ake ciki, mun ji a baya cewa kasa da mako guda bayan gwamnatin kasar Amurka ta sanya haramcin bayar da biza kan Najeriya da wasu kasashen Afrika, Zhou Pingjian, jakadan kasar China a Najeriya, ya ce ofishin jakadancin kasar ta dakatar da ba yan Najeriya biza.

Hakan, a cewarsa yana daga cikin kokarin da ake na magance cutar coronavirus da ya billo a kasar Asiya, jaridar The Nation ta ruwaito.

Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa sama da mutane dari uku ne suka mutu a kan mummunar annobar a China, yayinda kungiyar lafiya ta duniya ta kaddamar da shi a matsayin matsalar duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel