Yanzu Yanzu: Gwamnatin Edo ta bukaci kama Oshiomhole tare da hukunta shi cikin gaggawa

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Edo ta bukaci kama Oshiomhole tare da hukunta shi cikin gaggawa

- Gwamnatin jihar Edo ta nemi a kama Shugaban na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa Kwamrad Adams Oshiomhole tare da hukunta shi

- Mataimakin gwamnan jihar, Phillip Shuaibu ya ce zai gabatar da wani korafi ga Shugaban yan sanda da kuma hukumar tsaro na farin kaya don neman kama Oshiomhole

- Sai dai Shuaibu ya ce, har yanzu Oshiomhole mahaifinsa ne duk kuwa da cewar basa a babi guda ta fannin siyasa

Rikicin jihar Edo ta dauki sabon salo yayinda gwamnatin jihar ta nemi a kama tare da hukunta Kwamrad Adams Oshiomhole.

Jihar na so hukumomin tsaro su kama Shugaban na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa da kuma hukunta shi kan rashin bin umurnin gwamnatin jihar.

Mataimakin gwamnan jihar, Phillip Shuaibu ya fada ma manema labarai a Abuja cewa zai gabatar da wani korafi ga Shugaban yan sanda da kuma hukumar tsaro na farin kaya don neman kama Oshiomhole.

Sai dai Shuaibu ya ce, har yanzu Oshiomhole mahaifinsa ne duk kuwa da cewar basa a babi guda ta fannin siyasa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki, ya sha alwashin gasa wa tsohon gwamnan jihar kuma Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Comrade Adams Oshiomhole aya a hannu idan har ya cigaba da hargitsa ayyuka a jihar da kuma APC reshen Edo.

Gwamna Obaseki ya ce Oshiomhole ba zai taba lamuntan abunda shi yake lamunta na rashin da’a ba a lokacin da ya ke a matsayin gwamna.

KU KARANTA KUMA: Harkar fim tamkar kabari ce, idan an shiga ba a fita - Jamila Gamdare

Obaseki wanda ya yi magana a lokacin da ya halarci taron shugabannin kananan hukumomi 18 na APC a jihar ya ce zai nunawa Oshiomhole cewa shine gwamnan jihar.

Gwamnan na Edo ya ce APC reshen jihar na danasanin daukaka Oshiomhole ba tare da ta san irin mutumin da yake ba.

Ya umurci shugabannin jam’iyyar da su gallaza wa duk mutane ko kungiya da ke gudanar da ayyukan da suka saba ma yarjejeniyar jam’iyya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng