Auren zumunci na iya haddasa cutar kansar ido - Masana
Rahotanni sun kawo cewa masa a harkar lafiya sun ce akwai wani nau'in cutar kansar ido da auren zumunci ke iya haddasa wa.
An tattaro cewa tsohuwar babbar jami'ar shirin takaita cutar kansa ta Najeriya, Dr. Ramatu Hassan ce ta bayyana hakan a wata hira da shafin BBC a ranar Talata wanda ya yi daidai da ranar cutar Kansa ta Duniya.
A cewar Dr Ramatu auren zumunci ko na dangi da ake yi tsakanin mutane kan yi sanadiyar haifo yaro mai irin wannan lalurar.
Ta kara da cewa kasashen da ke da yawan auren zumunci kamar arewacin Najeriya na da yawan cutar.
Ta ce ''Irin wannan cuta ta kansar Ido na samuwa ga jarirai tun suna cikin ciki, saboda gado ake yi yawanci, kuma yana faruwa a inda ake yawan yin auren dangi, don haka akwai yiwuwar idan aka ci gaba da auren dangi to kuwa za a ci gaba da samun cutar.”
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Majalisar wakilai na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro
Cutar na fitowa ne a dai-dai inda ya kamata ido ya gani, sai a haifi yaro da ita a hankali a hankali tana ci gaba da girma, yayin da yaro ya kamata ya fara tafiya sai ya rika tuntube kamar yadda likitar ta bayyana.
A wani labari na daban, mun ji cewa hukumar 'yan sandan jihar Enugu ta yi wa wani miji kiran gaggawa bayan wata wallafa a kan shi da wani yayi.
Wani bawan Allah ya bukaci taimakon jama'a a shafin tuwita don neman mafita ga wata matar aure da mijinta yayi mata dukan kawo wuka.
Ba dukan bane sabon abu, don an saba cin zarafin mata ko ma'aurata a Najeriya. Dukan da yayi wa matar ne a wajen dinkin aikin da aka yi mata na cire da daga cikinta.
Bayan 'yar hatsaniyar da ta wanzu tsakanin ma'auratan, mijin ya kama matar inda ya lakada mata dukan kawo wuka tare da dukan wajen da aka yi mata aiki don cire da. Wannan lamarin kuwa yasa ta fadi rai a hannun Allah.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng