Yanzu Yanzu: Ofishin INEC na jahar Imo ta kama da wuta
- Ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ke Orlu, jahar Imo ta kama gobara
- Gobarar ta fara ne da misalin karf 6:00 na asuba daga wani daji da ke kusa da ofishin INEC a karamar hukumar Orlu da ke jahar Imo
- Daraktan hukumar kashe gobara a jahar, Japhet Okereafor, ya ce yana sane da lamarin amma babu kayan aiki
Ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ke Orlu, jahar Imo ta kama da wuta a ranar Litinin, 3 ga watan Fabrairu.
Jaridar The Sun ta ruwaito cewa gobarar ta fara ne da misalin karf 6:00 na asuba daga wani daji da ke kusa da ofishin INEC a karamar hukumar Orlu da ke jahar Imo.
Majiyoyi sun bayyana cewa babu mamaki gobarar ta kona wasu manoma a yankin sannan ya fi karfin mutane sakamakon yanayi na dari da ake ciki.
Da take tabbatar da lamarin, kakakin hukumar INEC a jahar, Emmanuella Opara, ta ce basu riga sun san yawan barnar da lamarin ya yi ba da kuma dalilin faruwar hakan.
“Kwarai muna iya tabbatar da cewar gobara ta kona ofishin INEC, amma ba za mu iya cewa ga yawan barnar da ya yi ko abunda ya haddasa ba sabboda bamu riga mun ziyarci wajen ba,” in ji Opara.
KU KARANTA KUMA: Harkar fim tamkar kabari ce, idan an shiga ba a fita - Jamila Gamdare
Har ila yau da ya ke magana, daraktan hukumar kashe gobara a jahar, Japhet Okereafor, ya ce yana sane da lamarin.
Okereafor ya bayyana cewa jami’an hukumar kashe gobara basu iya kashe wutar ba saboda rashin mota dama direban da zai tuka motar.
“Ina sane da batun gobarar amma babu isassun motoci kuma direba guda da muke dashi baya nan,” in ji Okereafor.
A wani labari na daban, mun ji cewa akalla mutane 245 suka rasa rayukansu a watan farkon shekarar 2020, rahotannin kashe-kashe da aka tattara ya bayyana hakan.
A cewar rahoton bincike da InterNations ta gudanar, Najeriya ce kasa mafi hadarin zama a duniya na uku bayan kasar Afghanistan da Syriya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng