Da dumi-dumi: Majalisar wakilai na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro

Da dumi-dumi: Majalisar wakilai na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro

- Shugabannin tsaro da ministan tasaro na cikin wata ganawar sirri a yanzu haka

- Daga cikin wadanda suka halarci ganawar harda kwamitin majalisar wakilai kan kwararru na kasa, rundunar sojin ruwa, rudunar sojin kasa, rundunar sojin sama da kuma tsaro, ana kuma sa ran kakakin majalisar ma zai zo

- Ganawar baya rasa nasaba da sammacin da majalisar wakilai ta aika a makon da ya gabata saboda tabarbarewar lamarin tsaro a kasar

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa a yanzu haka shugabannin tsaro da ministan tasaro na cikin wata ganawar sirri.

Daga cikin wadanda suka halarci ganawar harda kwamitin majalisar wakilai kan kwararru na kasa, rundunar sojin ruwa, rudunar sojin kasa, rundunar sojin sama da kuma tsaro.

Ana sanya ran kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ma zai kasance a ganawar wacce ke kan gudana a yanzu.

Da fari lokacin da Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu ya iso majalisar dokokin, kai tsaye ya wuce ofishin kakakin majalisar wakilan.

An tattaro cewa ganawar baya rasa nasaba da sammacin da majalisar wakilai ta aika a makon da ya gabata saboda tabarbarewar lamarin tsaro a kasar.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yiwa wani tsohon dan majalisa rasuwa jim kadan bayan kammala bikin zagayowar ranar haihuwarsa

A halin da ake ciki, a baya mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin da zai dinga duba halin da tsaron kasar nan ke ciki akai-akai.

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana hakan bayan ganawar da suka yi tare da shugaban kasar da kuma shugaban majalisar dattijan kasar nan.

Gbajabiamila ya sanar da manema labaran gidan gwamnati cewa 'yan kwamitin zasu hada ne da zababbu, 'yan majalisa da kuma 'yan jam'iyyar APC.

Ya ce kwamitin zai tallafa wajen shawo kan matsalar tsaron kasar nan baki daya.

A yayin da aka tambaye shi a kan yadda wasu daga cikin 'yan Najeriya suka bukaci a sauke shugabannin tsaron kasar nan, Gbajabiamila ya ce: "Ra'ayoyi sun rabu amma mafi rinjaye shine a saukesu. Wannan shine ya zamo abun tattaunawarmu a majalisar wakilai da dattijai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel