Sufeto Janar na yan sanda ya gurfana a gaban majalisar dattawa kan rashin tsaro

Sufeto Janar na yan sanda ya gurfana a gaban majalisar dattawa kan rashin tsaro

- Shugaban yan sandan Najeriya, Mohammed Aamu, ya gurfana a gaban majalisar dattawa kan hauhawan rashin tsaro a fadin kasar

- Hakan ya kasance amsa gayyatar da majalisar dattawa ta yi masa a makon da ya gabata

- Majalisar dattawa ta gayyacin Shugaban yan sandan don tattauna rashin tsaro na kasa, bukatar sauya fasalin tsaro a kasar da kuma manufar tsaro na jiha

Sufeto janar na yan sanda, Mohammed Aamu, ya gurfana a gaban majalisar dattawa kan hauhawan rashin tsaro a fadin kasar.

Bayyanar nasa ya kasance amsa gayyatar da majalisar dattawa ta yi masa a makon da ya gabata.

Sufeto Janar na yan sanda ya gurfana a gaban majalisar dattawa kan rashin tsaro
Sufeto Janar na yan sanda ya gurfana a gaban majalisar dattawa kan rashin tsaro
Asali: UGC

Mista Adamu ya isa zauren majalisa da misalin karfe 11:08 na safe tare da wasu jami’an tsaro da suka yi masa rakiya.

Majalisar dattawa ta gayyacin Shugaban yan sandan don tattauna rashin tsaro na kasa, bukatar sauya fasalin tsaro a kasar da kuma manufar tsaro na jiha.

Yan majalisar dokoki sun sadaukar da Talatar da ya gabata kacokan don tattauna lamarin. Yayinda Shugaban marasa rinjaye a majalisa, Enyinnaya Abaribe ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi murabus a matsayin Shugaban kasa, majalisar dattawan ta nemi ya salami shugabannin tsaron sannan ya nada sabbi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: An gurfanar Hamisu Wadume da Kyaftin Balarabe a kotu

Har ila yau majalisar dattawan ta kafa kwamitin wucin-gadi don tattaunawa da hukumomin tsaro da neman hanyoyin kawo karshen annobar.

A halin da ake ciki, mun ji cewa a yanzu haka shugabannin tsaro da ministan tasaro na cikin wata ganawar sirri.

Daga cikin wadanda suka halarci ganawar harda kwamitin majalisar wakilai kan kwararru na kasa, rundunar sojin ruwa, rudunar sojin kasa, rundunar sojin sama da kuma tsaro.

Ana sanya ran kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ma zai kasance a ganawar wacce ke kan gudana a yanzu.

An tattaro cewa ganawar baya rasa nasaba da sammacin da majalisar wakilai ta aika a makon da ya gabata saboda tabarbarewar lamarin tsaro a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel