Yan sanda sun cafke manyan masu garkuwa da mutane su 4 a hanyar Abuja-Lokoja

Yan sanda sun cafke manyan masu garkuwa da mutane su 4 a hanyar Abuja-Lokoja

- Jami'an yan sandan birnin tarayya sun kama wasu masu garkuwa da mutane su hudu a yammacin ranar Lahadi a kauyen Piri, kusa da Kwali, a hanyar Abuja-Lokoja

- Yan sandan sun amsa kira ne bayan masu garkuwan sun harbi wata motar bus kirar Toyota Previa sau da dama sannan suka yi garkuwa da wasu fasinjojin motar bayan sun tsayar da bus din ta karfin tsiya

- Sunayen wadanda yan sanda suka kama sune; Shuaibu Sule, 27, Mohammadu Usman, 25, Umar Usman, 19, da kuma Usman Ibrahim, 20

Rundunar yan sandan birnin tarayya ta kama wasu masu garkuwa da mutane su hudu a yammacin ranar Lahadi a kauyen Piri, kusa da Kwali, a hanyar Abuja-Lokoja.

Kakakin yan sandan birnin tarayya, DSP Anjuguri Manzah a Wani jawabi da ya saki a ranar Litinin, ya ce jami’an rundunar sun kama masu laifin hudu bayan sun amsa wani kira mai cike da damuwa a ranar Lahadi da misalin karfe 5:30.

Ya ce masu garkuwan sun harbi wata motar bus kirar Toyota Previa sau da dama sannan suka yi garkuwa da wasu fasinjojin motar bayan sun tsayar da bus din ta karfin tsiya.

Yan sanda sun cafke manyan masu garkuwa da mutane su 4 a hanyar Abuja-Lokoja
Yan sanda sun cafke manyan masu garkuwa da mutane su 4 a hanyar Abuja-Lokoja
Asali: Twitter

Ya ce tawagar yan sanda da ke sintiri sun fafata da masu garkuwan inda suka sha karfinsu.

“Yayinda yan sanda da wasu matasa a garin da ke kusa suka ceto wasu fasinjoji har yanzu sauran na a hannun masu garkuwan,” in ji shi.

Ya bayar da sunayen wadanda yan sanda suka kama a matsayin Shuaibu Sule, 27, Mohammadu Usman, 25, Umar Usman, 19, da Usman Ibrahim, 20.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ba za mu kara farashin tikitin jirgin kasa ba – Amaechi

A cewarsa an kwato bindiga daya, adduna, da AK 47.

Manzah ya ce rundunar na kokarin ceto wadanda masu garkuwan suka sace.

A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta shawarci makarantu, wuraren bauta, kasuwanni, tashar motoci da sauran wuraren da jama'a ke taruwa da su dawo da salon duba kayan mutane kafin barinsu shiga.

Wannan shawarar ta biyo bayan kama wani mutum da ake zargin dan kunar bakin wake mai suna Nathaniel Samuel, a cocin Living Faith da ke Sabon Tasha Kaduna, a ranar Lahadi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel