Bayan Shekara 1 da Harin Yelewata, Lakurawa Sun Kashe fiye da Mutane 15 a Kebbi

Bayan Shekara 1 da Harin Yelewata, Lakurawa Sun Kashe fiye da Mutane 15 a Kebbi

  • Wasu da ake zargin ‘yan Lakurawa ne sun kashe akalla mutane 20 a kauyen Fasken Rafi da ke jihar Kebbi ranar Lahadi
  • Harin ya faru shekara guda bayan kisan gillar Yelewata a Benue inda sama da mutane 200 suka rasa rayukansu
  • Shugabanni da malaman addini sun bukaci gwamnati ta dauki matakin gaggawa domin dakile kashe-kashe da matsalar tsaro a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kebbi - Sababbin hare-hare da kashe-kashe a wasu sassan Najeriya sun sake tayar da hankula kan tabarbarewar matsalar tsaro a kasar.

Lamarin ya kara daukar hankali ne bayan wasu da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne sun kai hari kauyen Fasken Rafi da ke karamar hukumar Arewa a jihar Kebbi.

An yi taron tunawa da mutanen da aka kashe a Yelewata.
Mutane sun taru a Yelewata don tunawa da mutanen da aka kashe a 2025. Hoto: Ben Atonko
Source: Facebook

Lakurawa sun kashe mutum 20 a Kebbi

Mazauna yankin sun bayyana harin a matsayin daya daga cikin mafi muni da aka kai yankin cikin ‘yan kwanakin nan, inda aka kashe kalla mutane 20 kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a Ukraine bayan Rasha ta harba daruruwan jiragen yaki

Harin ya zo ne shekara guda bayan kisan gillar da aka yi a Yelewata da ke karamar hukumar Guma a jihar Benue, inda sama da mutane 200 suka mutu tsakanin ranar 13 zuwa 14 ga watan Yunin 2025.

Mahukuntan jihar Kebbi sun tabbatar da aukuwar harin, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta tura wata tawaga karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Umar Tafida, zuwa yankin da abin ya shafa.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Tafida ya yi alkawarin kara karfafa ayyukan jami’an tsaro a yankin domin hana sake aukuwar irin harin.

“Wannan rashin rayuka abin takaici ne sosai. Gwamnatinmu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyi,” in ji Tafida.

Ya kara da cewa gwamnati za ta tura karin jami’an tsaro da kayan aiki domin dakile hare-haren da ake fama da su a yankin.

Sarkin Argungu ya ba da shawarar kare kai

Harin ya faru ne kwanaki bayan Sarkin Argungu, Mohammad Samaila Mera, ya bukaci al’ummomin da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga su nemi lasisin mallakar makamai bisa doka domin kare kansu.

Basaraken ya ce ya kamata al’umma su hada kai su samo hanyoyin kare kansu cikin tsarin doka, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

ESN ta shirya kai hare hare a wasu sassan Najeriya, DSS, sojoji sun dauki mataki

A cewarsa, idan maharan sun san cewa al’umma na da kayan kare kai, hakan ka iya rage yawan hare-haren da ake kai musu.

'Yan ta'addar Lakurawa sun kashe akalla mutane 20 a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, inda ake fargabar Lakurawa sun hallaka akalla mutane 20. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An tuna da wadanda aka kashe a Yelewata

A lokaci guda kuma, al’umma da shugabanni a jihar Benue sun gudanar da taron tunawa da wadanda aka kashe a harin Yelewata na shekarar 2025.

An gudanar da bikin ne yayin kaddamar da wani abin tunawa da aka gina domin girmama wadanda suka mutu a harin, cewar rahoton Leadership.

Yayin taron, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Patrick Abba Moro, ya soki wamnatin tarayya da ‘yan siyasa kan yadda suke tafiyar hawainiya wajen magance matsalar tsaro.

Ya ce kin amincewa da girman matsalar na daga cikin abubuwan da suka sa hare-hare ke ci gaba da yawaita.

An kashe mutane da yawa a Kebbi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe mutane takwas a kauyukan Kaiwa da Gebbe na jihar Kebbi, sannan sun cinna wa gidan shugaban gari wuta.

Hare-haren sun tilasta wa daruruwan mazauna yankin tserewa zuwa garin Shanga bayan barin saboda tsananin tsoro da fargaba.

Rundunar yan sandan ta ce jami'an tsaro sun fara gudanar da sintiri na musamman domin kamo 'yan ta'addar da suka aikata laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com