Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin Kano ta tsige Shugaban masu rinjaye

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin Kano ta tsige Shugaban masu rinjaye

- An tsige Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano, Lawan Abdul-Madari

- Hakan ya biyo bayan amincewar mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) 23 cikin 28 da ke majalisar

- Har ila yau an maye gurbin Mista Abdul-Madari da Kabiru Hassan-Dashi

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an tsige Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano, Lawan Abdul-Madari.

An maye gurbin Mista Abdul-Madari da Kabiru Hassan-Dashi.

Mamba mai wakiltan karamar hukumar Bunkure a majalisar, Uba Gurjiya ne ya daukaka takardar sanar da tsigewar.

Mista Gurjiya ya daukaka bukatar ne a madadin yan majalisar na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 23 cikin 28 a majalisar.

A ranar Talata dai aka rantsar da Gurjiya a matsayin dan majalisa a zaman majalisar karkashin jagorancin kakakinta, Abdulazeez Garba-Gafasa, biyo bayan nasarar da ya samu a zaben da aka sake kwanan nan a jihar.

A cewarsa, an yanke shawarar tsige Shugaban masu rinjayen ne biyo bayan wata yarjejeniya da yan majalisa na APC su 23 cikin 28 a majalisar suka yi.

Batun tsigewar ya samu goyon bayan wani dan APC da ke wakiltan Bagwai/Shanono, Ali Shanono.

Biyo bayan aiwatar da lamarin, yan majalisar sun yi kira ga Shugaban masu rinjayen da ya ja gefe.

Bayan tsige Shugaban masu rinjayen, wani dan majalisa na APC mai wakiltan mazabar Sumaila, Hamza Masu, ya zabi mataimakin Shugaban masu rinjaye don maye gurbin Madari.

Sai wasu yan majalisa suka goti bayan hakan sannan majalisar ta aiwatar.

KU KARANTA KUMA: Sufeto Janar na yan sanda ya gurfana a gaban majalisar dattawa kan rashin tsaro

Yan majalisar ba su ambaci wani kwakkwaran dalili na aikata hakan ba. Sai dai kuma a zaman karshe da suka yi, tsohon Shugaban masu rinjayen ya yi gaba-da-gaba dda takwarorinsa, inda ya yi adawa da zabar wani sakataren din-din na sakatariyar ilimi na karamar hukuma wanda sauran yan majalisar suka amince da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel