An Fille Kan Wata Mata a Birnin Tarayya Abuja, Mutane Sun Shiga Tashin Hankali

An Fille Kan Wata Mata a Birnin Tarayya Abuja, Mutane Sun Shiga Tashin Hankali

  • Mazauna yankin Bwari a Abuja sun gano gawar wata mata mai matsakaicin shekaru ba tare da kai ba a wani gini da ba a kammala ba
  • Rahotanni sun nuna cewa warin da ke fita daga ginin ne ya sa mutane suka shiga ciki suka gano gawar matar da aka fille wa kai
  • Rundunar ‘yan sanda ta kwashe gawar zuwa asibiti tare da fara bincike domin gano ko wacece da yadda aka kashe ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Mazauna yankin Bwari da ke Babban Birnin Tarayya Abuja sun shiga cikin firgici bayan gano gawar wata mata a wani gini da ba a kammala ba.

Rahotanni sun nuna cewa an gano gawar matar ne a ranar Asabar, kuma an cire mata kai.

An gano gawar wata mata babu kai a wani kango a Abuja
Jami'an tsaro sun kwashe gawar matar da aka fille wa kai a Abuja. Hoto: UGC
Source: UGC

An gano wata mata babu kai a Abuja

Kara karanta wannan

Tinubu zai kashe Naira tiriliyan 5 kan tsaro, za a dauki sababbin ƴan sanda 50000

Mutanen yankin sun ce sun fara zargin akwai matsala ne bayan sun ji wani mummunan wari na fita daga ginin da aka dakatar da aikinsa, in ji rahoton Daily Trust.

Hakan ya sa wasu mazauna yankin suka shiga cikin ginin domin gano abin da ke faruwa kafin daga bisani suka tarar da gawar matar.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce yanayin gawar ya nuna cewa an kashe matar ne kwanaki kafin a gano ta.

A cewarsa, warin da ke fita daga ginin ne ya jawo hankalin mutane, inda ya ce:

“Da muka shiga cikin ginin, sai muka tarar da gawar matar ba tare da kai ba.”

Yanayin da aka ga gawar matar

Wani mazaunin yankin ya kuma yi zargin cewa akwai alamun da ke nuna an daure matar kafin kashe ta.

Ya ce an ga igiyoyi a jikin gawar tare da wani bargo da ake kyautata zaton an yi amfani da shi wajen ɗaukar gawar.

Yayin da ya ce yanayin gawar ya nuna cewa matar ta yi ƙoƙarin kare kanta kafin a kashe ta, ya kuma bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Amurka ta jefa makamai, an hallaka jami'an kasar Indiya

“Ba mu iya gane ko wace ce ba saboda babu kai a jikinta. Haka kuma an ga alamun da ke nuna ta yi turje turje kafin mutuwarta.”

Wasu mazauna yankin sun bayyana lamarin a matsayin abin tsoro tare da nuna damuwa kan matsalar tsaro da ke ƙaruwa a yankin.

Majiyar 'yan sanda ta ce an kwashe gawar matar zuwa asibiti domin fara bincike.
Kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh. Hoto: @jossyadeh
Source: Twitter

‘Yan sanda sun fara bincike

Jami’an rundunar ‘yan sanda daga hedikwatar Bwari sun isa wurin bayan samun rahoton lamarin, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Wani jami’in ‘yan sanda da ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun samu kiran gaggawa daga wani mazaunin yankin a ranar Asabar.

Ya bayyana cewa an kwashe gawar zuwa Babban Asibitin Bwari domin ci gaba da bincike. A cewarsa, rundunar ta fara bincike domin gano ko wacece matar da kuma yadda aka kashe ta.

An fille kan 'yar shekara 69

A wani labari, mun ruwaito cewa, ’yan sanda a Anambra sun kama Obadigbo Emmanuel Anumudu da ake zargi da fille kan wata mata mai shekara 69.

An kama shi ne bayan shekara guda da ya gudu daga yankin Umueri, inda aka kashe Obianuju Akubi a watan Yulin 2024.

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ’yan sanda ta ce bincike yana ci gaba da gudana domin kama sauran masu hannu a laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com