Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an saki yaran wani likita mazaunin Kaduna, Philip Ataga wadanda aka yi garkuwa da su a watan Janairu. An saki yaran ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu.
Babbar kotun Kaduna, ta ba Shugaban kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi na Shi’a, Sheikh Ibrahim el-Zakzaky da matarsa, Zeenat, damar ganin Likitocin su don su sami damar iya bayyana a gaban kotun a zamanta na gaba.
Koda dai an kammala zaben kasa kuma akwai sauran lokaci sosai kafin a sake wani zabe na gaba, har yanzu lamuran siyasa na daga cikin manyan batutuwan da ake tattaunawa yayinda yan siyasa ke bin hanyoyin kafa kansu.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi karin haske kan 'yan bindigar kungiyar Ansaru 250 da ta yi ikirarin cewa ta kashe a wani mamaya da suka kai jahar Kaduna.
Mahaifiyar jarumar mai suna Hajiya Maryam Yusuf ta amsa kiran mahaliccinta a safiyar yau Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, a wani asibitin Abuja bayan ta sha fama da jinya na tsawon lokaci.
A wani bidiyo da hirar WhatsApp da ke ta yawo a shafukan sadarwa, an gano cewa wani matashi ya yi kokarin siyan wayoyin iPhone 11 pro guda biyu da alat na bogi.
Gwamna Babagana Umara Zulum na jahar Borno, ya ziyarci yankin Monguno inda ya kwashe tsawon kwana biyu a garin. Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi daga hadimin gwamnan kan harkokin labarai, Isa Gusau ya fitar a ranar Laraba.
Sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya bukaci gwamnonin jahohi da su sauke hakkin da ya rataya a wuyansu, cewa wadanda ke aikata laifuffuka na da dalilansu na aikata hakan.
Hankula na nan sun tashi a yankunan Aboru da Iyana Ipaja na jihar Lagas yayinda masu sana’ar tuka babur ke zanga-zanga akan ayyukan wata kungiyar tsaro kan muhalli da sauran laifuffuka masu alaka.
Aisha Musa
Samu kari