Masu garkuwa da mutane sun saki yaran wani likitan Kaduna bayan sun kashe mahaifiyarsu

Masu garkuwa da mutane sun saki yaran wani likitan Kaduna bayan sun kashe mahaifiyarsu

- Masu garkuwa da mutane sun saki yaran wani likita mazaunin Kaduna, Philip Ataga da suka sace a watan Janairu

- An yi garkuwa da yaran wadanda aka bayyana a matsayin Christabel da Jasmine tare da mahaifiyarsu a yankin Juji na karamar hukumar Chikun da ke jahar Kaduna a ranar 25 ga watan Janairu

- Sai dai dama yan bindigan sun kashe mahaifiyar yaran saboda rashinbiyan kudin fansa

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an saki yaran wani likita mazaunin Kaduna, Philip Ataga wadanda aka yi garkuwa da su a watan Janairu.

An saki yaran ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, Channels TV ta ruwaito.

An yi garkuwa da yaran wadanda aka bayyana a matsayin Christabel da Jasmine tare da mahaifiyarsu a yankin Juji na karamar hukumar Chikun da ke jahar Kaduna a ranar 25 ga watan Janairu.

Masu garkuwa da mutane sun saki yaran wani likitan Kaduna bayan sun kashe mahaifiyarsu
Masu garkuwa da mutane sun saki yaran wani likitan Kaduna bayan sun kashe mahaifiyarsu
Asali: Twitter

Da farko masu garkuwan sun nemi a biya su fansar naira miliyan 150 a matsayin kudin kasar sakinsu amma suka kashe mahaifiyar yaran bayan an ki biyansu kudin.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya bayyana a makon da ya gabata cewa an gano gawar matar wanda ke dauke da harbi a wani daji a yankin Kakau hanyar babban titin Abuja zuwa Kaduna.

KU KARANTA KUMA: An kashe dan Najeriya saboda kawai yayi fitsari akan titi a kasar Amurka

Koda dai rundunar yan sandan bata riga ta tabbatar das akin yaran biyu ba, mahaifinsu Dr Philip ya bayyana wa majiyarmu cewar masu garkuwan sun ajiye yaran a yankin Unguwar Kati hanyar titin Jeji inda daga bisani wani dan uwansa ya je ya kwashe su zuwa gida.

Sai dai bai bayyana ko an biya kudin fansar kafin sakin yaran ba.

A wani lamari na daban, mun ji cewa wani mutum mai suna Auwallu Abdullahi mai shekaru 25 da budurwasa mai shekaru 19 an tsinci gawarsu a dakin janareto a Unguwar Gaya da ke yankin Badawa a cikin birnin Kano.

Ana zargin masoyan biyu sun mutu ne sakamakon hayakin janareton bayan sun kulle kansu a dakin Janareton na dogon lokaci. Lamarin ya faru ne wajen karfe 9 na dare a ranar Laraba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel