An fitar da sunayen hatsabiban 'yan fashin da 'yan sanda suka kashe a Kaduna

An fitar da sunayen hatsabiban 'yan fashin da 'yan sanda suka kashe a Kaduna

- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi karin haske kan 'yan bindigar kungiyar Ansaru 250 da ta yi ikirarin cewa ta kashe a wani mamaya da suka kai jahar Kaduna

- Hatsabiban yan fashin da aka kama kuwa su ne Haruna Basullube da Bashir Leta

- Yan sandan sun kuma yi wa wani kwamandan kungiyar Boko Haram, Malam Abba da wani hatsabibin mai garkuwa da mutane, Mofa, mummunan rauni

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi karin haske kan 'yan bindigar kungiyar Ansaru 250 da ta yi ikirarin cewa ta kashe a wani mamaya da suka kai jahar Kaduna.

A ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairu ne rundunar Operation Puff Adder ta ce jami'anta sun kai farmaki a dajin Kuduru da ke Birnin Gwari a jihar ta Kaduna tare da taimakon sojojin sama.

Sai dai rundunar ta kara da cewa an harbi wani jirginta mai saukar ungulu a lokacin harin.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu ta ce jami'anta sun kashe wasu hatsabiban masu fashi a daji da masu satar shanu da garkuwa da mutane da take nema ruwa a jallo.

Wadannan yan fashin kuwa su ne Haruna Basullube da Bashir Leta, shafin BBC ta ruwaito.

Har ila yau ta kara da cewa jami'anta sun kuma yi wa wani kwamandan kungiyar Boko Haram, Malam Abba da wani hatsabibin mai garkuwa da mutane, Mofa, mummunan rauni.

A cewarsu, an kwace bindigogi kirar AK47 da daruruwan harsasan manyan bindigogi masu jigida da kakin sojoji da manyan kwalayen kwayar Tramadol da wasu na'urori daga sansanonin.

KU KARANTA KUMA: Kano: An samu gawar wani saurayi da budurwa tsirara cikin wani gida

Rundunar 'yan sandan ta kuma tura jami'ai na musamman domin zurfafa bincike ta hanyar zamani kan ayyukan kungiyoyin da mukarrabansu.

A wani lamarin kuma mun ji cewa manyan hafsoshin tsaron kasa sun bayyana ma majalisar wakilai cewa akwai hannun kasashen waje a cigaba da ruruwar matsalolin tsaro a Najeriya, musamman matsalar ta’addanci da sauran kalubalen tsaro.

Daily Trust ta ruwaito manyan hafsoshin tsaron sun bayyana haka ne yayin wata ganawar sirri da suka yi da kwamitin tsaro ta majalisar wakilai, kamar yadda shugaban kwamitin, Babajimi Benson ya bayyana ma manema labaru.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng