Yan Bindiga Sun Hana Noma a Sokoto, Sun Saka wa Jama'a Haraji
- Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindiga sun hana mazauna wasu yankunan Sokoto zuwa gonaki, sun ƙaƙaba musu sababbin haraji
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da korafi game da matsalolin tsaro da suka addabi sassan Najeriya da dama
- Mazauna jihar Sokoto sun bayyana cewa 'yan bindiga suna iya sake dawowa su bukaci karin kudi ko sun biya harajin a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Mazauna aƙalla ƙauyuka 26 a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto sun fara tara kuɗi domin biyan sababbin harajin da ‘yan bindiga suka ƙaƙaba masu.
Harajin da 'yan ta'addan suka sanya ya zo ne bayan hana mutanen yankunan zuwa gonakinsu yayin da ake shirin fara noman damina.

Source: UGC
Mazauna yankin sun shaida wa Daily Trust cewa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun ba su wa’adin kwanaki uku, suna gargaɗin manoma da kada su je gonakinsu har sai an biya harajin da aka nema daga ƙauyukan da abin ya shafa.
Ƙauyukan Sokoto da aka sawa haraji
A cewar majiyoyin, ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Garin Faji, Cina Barka, Zululu, Dan Gari, Garin Maigayya, Gardi, Katsira, Garin Baushe, Sulmawa, Zakin Ganga da kuma Dan Kware.
Sauran sun hada da Garje, Dogon Faru, Son Allah, Garin Galadima, Kafchi, Matabaya, Garin Labo, Zango, Kaifin Aska, Tsauna Dogo, Tudun Wada, Rambadawa, Ga Itace, Nasarawa da Garin Idi.
Wani mazaunin yankin da ke da kusanci da mutanen ƙauyukan da abin ya shafa ya ce ‘yan bindigar sun yi barazanar kashewa ko sace duk wanda aka samu yana noma a wannan lokaci.
“An ba ƙauyukan wa’adin kwanaki uku. Sun ce babu wanda zai je gona har sai an biya kuɗin. Duk wanda aka kama yana noma ko dai a kashe shi ko a yi garkuwa da shi, kuma ba zai samu ‘yanci ba har sai an biya fansar N500,000,”
In ji shi.
An fara tara wa 'yan bindiga haraji
Mutumin ya ce mazauna yankin sun riga sun fara tara kuɗin domin biyan buƙatun masu garkuwa da mutanen da suka masu barazana.
Wani mazaunin ƙauyen Zululu, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yana shirin zuwa gonarsa ranar Juma’a ne lokacin da ya ji umarnin.
“An gaya mana cewa ‘yan bindigar sun hana ayyukan noma na kwanaki uku har sai ƙauyukan sun biya harajin da suke ƙaƙaba mana duk shekara.
“Sun ce da ma za su iya barin mutane su je gonaki sannan su kashe wasu su kuma yi garkuwa da wasu, amma sun fi son kuɗin.
"A cewarsu, jami’an tsaro suna ƙwace musu dabbobi, saboda haka ba za a yi noma ba har sai an biya harajin,”
In ji shi.

Source: Original
Sarakuna za su gana da 'yan bindiga
Ya ce ana sa ran sarakunan gargajiya da malaman addini daga ƙauyukan da abin ya shafa za su gana da ‘yan bindigar domin tantance adadin kuɗin da kowace al’umma za ta biya kafin a ci gaba da noma.
Mazaunin ya ce shekaru da dama kenan ana tilasta musu irin waɗannan biyan kuɗi ba tare da wata hujja ba.
Bayanin 'yan sandan Sokoto
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce rundunar ba ta da masaniya kan lamarin.
Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa a lokuta mafi yawa mutanen kauyuka ba su kawo irin rahotannin ga jami'an tsaro.
Gargadin da Janar Tukur Buratai ya yi
A wani labarin, kun ji cewa tsohon hafsan sojin kasa, Tukur Buratai (mai ritaya), ya yi gargaɗin cewa matsalar rashin tsaro a Najeriya na iya ƙara taɓarɓarewa.
Tukur Buratai ya ce shugabannin siyasa ciki har da ministoci, sanatoci da gwamnoni na iya fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane idan lamarin ya cigaba.
Ya yi wannan gargaɗi ne a cikin wata sanarwa mai taken “shawara ta gaskiya da kishin ƙasa kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a Najeriya” bayan rasuwar Janar Rabe Abubakar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


