Babu abinda zan iya yi kan karin harajin katin kiran waya – Pantami

Babu abinda zan iya yi kan karin harajin katin kiran waya – Pantami

- Sheikh Ali Pantami, ministansadarwa na kasa ya bayyana cewa ba zai iya cewa komai ba a kan harajin da aka kara a kudin kira na wayar salula

- Pantami ya ce batun karin harajin da aka yi ba a karkashin ofishinsa ya ke ba

- Ya roki masu korafi a kan lamarin da su kai kukansu hukumar tara haraji ta kasa wato FIRS

Ministan Sadarwa na Najeriya, Sheikh Ali Pantami ya bayyana cewa ba zai iya cewa komai ba a kan harajin da aka kara a kudin kira na wayar salula.

A cewar Pantami, batun karin harajin da aka yi ba a karkashin ofishinsa ya ke ba.

Ya ce: “Ma’aikatar sadarwa bata da ikon kara kudin katin kira ko saka haraji a kira. Hakan yana karkashin hukumar tara haraji ta kasa ce.”

Babu abinda zan iya yi kan karin harajin katin kiran waya – Pantami
Babu abinda zan iya yi kan karin harajin katin kiran waya – Pantami
Asali: Facebook

Ya roki masu korafi a kan lamarin da su garzaya hukumar tara haraji ta kasa wato FIRS domin mika kukan su.

‘Yan Najeriya na kokawa game da karin haraji da gwamnati ta yi akan kudin kira a wayan selula a kasar nan.

Sai dai kuma ma’aikatan a cikin wannan makon ya kafa sabbin sharuddan mallakar layi a kasar nan.

Wadannan sharuda sune kamar haka:

1. A rika yin rajista bisa Dokar Sadarwa ta 2003, mai lamba 25, Sashe na 25.

2. Duk wanda zai yi rajistar sabon layi, tilas sai ya bada lambar Shaidar Katin dan Kasa (NIN).

3. Duk wani dan kasar waje da ya shigo Najeriya, idan zai mallaki layin waya, tilas sai ya hada da lambar fasfo da ta biza din sa.

4. Sai nan da ranar 1 Ga Disamba za a kulle uzurin rashin yin wannan rajista.

5. Ba a yarda mutum daya ya mallaki layukan waya fiye da uku ba.

KU KARANTA KUMA: Ba zan goyi bayan Buhari ba idan zai sake zarcewa a karo na uku - Shekarau

6. Duk lambar da jami’an tsaro suka tabbatar da an taba aikata laifi da ita, to za a kulle ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel