Wani matashi ya shiga hannu bayan ya yi kokarin siyan wayoyin iPhone 11 Pro guda biyu da alat na bogi

Wani matashi ya shiga hannu bayan ya yi kokarin siyan wayoyin iPhone 11 Pro guda biyu da alat na bogi

- Wani mutum da ya yi ikirarin cewa sunansa Akeem ya gurfana bayan ya yi kokarin damfarar masu siyar da wayoyi

- An kama Akeem ne bayan ya yi kokarin siyan wayoyin ipone 11 Pro guda biyu da Kararrawar banki na bogi

- Akeem ya roki wadanda suka zarge sa da kada su bari ya koma gidan kurkuku yayinda ya yi ikirarin cewa bai dade ba da aka sake shi

Matakin da rashin tsaro ya kai a kasar ya kasance dalilin da yasa mutane ke takatsantsan sosai da junansu. Wasu mutane sun gwammaci su damfari mutane kudaden da suka samu da guminsu maimakon su yi aiki da karfinsu don samun nasu kudin.

Legit.ng ta gano wani rahoto na wani matashi wanda aka kama bayan ya yi kokarin siyan sadadden wayar hannu da Kararrawar banki na bogi.

A wani bidiyo da hirar WhatsApp da ke ta yawo a shafukan sadarwa, an tattaro cewa wani matashi ya yi kokarin siyan wayoyin iPhone 11 pro guda biyu da Kararrawar banki na bogi.

Bayan an kama shi, sai matashin wanda ya yi ikirarin cewa sunansa Akeem, ya tsuguna a kan gwiwowinsa yana rokon wanda ya yi wa sata da kada ya hukunta shi.

Akeem ya yi rokon cewa kwanan nan aka sake shi daga gidan yari kuma ba zai so sake komawa can ba.

A hirar WhatsApp da aka yada tare da bidiyon, wani mutum da Akeem ya so damfara a baya ya yi ikirarin cewa matashin shahararren makaryaci ne sannan cewa ya yi kokarin yi masa wayo a baya.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe mutane 3 a sabon harin da aka kai kan Kaduna

Mutumin ya kara da cewa Akeem bai je gidan yari ba a baya kamar yadda ya yi ikirari sannan cewa shakka babu killan da suna na bogi ya ke amfani. Sannan kuma cewa babu ta yadda za su san ko gaskiya ya ke fadi.

Allah ya kyauta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel