Janar Rabe: Buratai Ya Yi Gargadi kan 'Sace' Gwamnoni da Ministoci a Najeriya
- Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya) ya yi gargaɗin cewa matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a Najeriya na iya ƙara muni idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba
- Buratai ya ce shugabannin siyasa ciki har da ministoci, sanatoci da gwamnoni na iya fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya
- Ya ba da shawarar kafa hukumar gaggawa ta kasa wadda za ta kasance da cikakken iko kan dukkan hukumomin tsaro da ke aiki a yankunan da ke cikin haɗari a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya yi gargaɗin cewa matsalar rashin tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a Najeriya na iya kai wa ga manyan masu riƙe da muƙaman siyasa.
Tukur Yusuf Buratai ya ce cikin wadanda za a iya kai wa hari ciki har da ministoci, sanatoci da gwamnonin jihohi, idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.

Source: Facebook
Tribune ta rahoto cewa Buratai ya yi wannan gargaɗi ne a cikin wata sanarwa da aka bai wa manema labarai a ranar Lahadi yayin da yake mayar da martani kan mutuwar Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya).
Buratai ya yi gargadin yiwuwar sace ministoci
A cewar Buratai, mutuwar babban jami’in soja ya nuna raguwar ƙarfin da ake da shi a fagen tsaro kuma hakan babbar barazana ce ga tsaron ƙasa.
“Bari na bayyana a sarari: idan aka bar wannan al’amari ya ci gaba ba tare da an dakatar da shi ba, waɗanda za a kai wa hari a gaba ba sojoji ko fararen hula kaɗai ba ne.
"Zai iya haɗawa da ministoci, sanatoci har ma da gwamnonin jihohi. Babu wani shugaba da zai tsira,”
In ji Buratai.
Bayani kan hasashen da aka yi
Buratai ya tunatar da cewa tun a shekarar 2021 ya yi hasashen cewa tada ƙayar baya da ayyukan ‘yan bindiga na iya ci gaba har tsawon shekaru 20 idan ba a ɗauki matakai masu ƙarfi ba.
Leadership ta rahoto ya ce:
“Yau, ƙasarmu na ganin yadda wannan hasashe ke cika a zahiri. Kama, azabtarwa da kuma kashe babban jami’in soja, Manjo Janar Rabe Abubakar, ya nuna an tsallaka wani mataki mai haɗari,”
'Yan bindiga sun kara dabaru
Tsohon hafsan sojin ya ce yanzu ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya suna da hanyoyin tattara bayanan sirri, makamai na zamani da kuma kara ƙarfin hali.
Ya soki abin da ya kira tsarin mayar da martani kawai ga matsalar rashin tsaro, ciki har da biyan kuɗin fansa da tattaunawa da masu laifi, yana mai cewa dole ne a kawo ƙarshen irin waɗannan dabaru.

Source: Twitter
Ya kuma ba da shawarar amfani da tsari irin na Kwamitin shugaban kasa kan COVID-19, inda za a samu tsarin jagoranci guda ɗaya da zai kula da ayyukan tsaro a jihohin da ke cikin haɗari.
'Janar Rabe bai da ciwon sukari'
A wani labarin, kun ji cewa daya daga cikin ‘ya’yan marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), Isyaka Rabe, ya ƙaryata cewa yana da ciwon sukari.
Gwamnatin jihar Katsina ta ce mahaifinsu ya mutu ne sakamakon matsalolin ciwon suga da hawan jini yayin da 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi.
A wata hira da aka yi da shi a ranar Lahadi, Isyaka ya bayyana rahotannin da ke cewa mahaifinsa ya mutu sakamakon ciwon suga a matsayin marasa inganci.
Asali: Legit.ng


