Bidiyon tsaraicin Maryam Booth: Ana farautar wasu mutane 2

Bidiyon tsaraicin Maryam Booth: Ana farautar wasu mutane 2

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa shugabannin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood su na taimaka wa jami'an tsaro don cafke wasu mutane biyu da ake zargi da daukar wani bidiyo na fitacciyar jarumar masana’antar Maryam Booth tsirara tare da yada shi a shafukan zumunta.

Tun daga jiya Alhamis, 7 ga watan Fabrairu ne guntun bidiyon ya bulla inda ya fara yawo gadan-gadan a gari.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa shekara uku kenan da aka dauki wannan bidiyo da ke yawo a gari.

A gajeren bidiyon dai, an gano kyakkyawar jarumar ta Kannywood tsirara timbir a cikin daki kamar ta fito daga wanka. Babu komai a jikin ta sai kallabi a kan ta.

Bidiyon tsaraicin Maryam Booth: Ana farautar wasu mutane 2
Bidiyon tsaraicin Maryam Booth: Ana farautar wasu mutane 2
Asali: Twitter

Akwai tabbacin cewa wanda ya yi bidiyon ya dauke ta ne da gangan, ba tare da amincewar ta ba, domin kuwa da ta ankara ana ɗaukar ta sai ta yi wuf ta kwace wayar da ake ɗaukar ta da ita.

Har ila yau mujallar fim ta rahoto cewa shugaban kungiyar jaruman Kannywood ta Jihar Kano, Malam Alhassan Kwalle, ya tabbatar mata cewa kungiyar sa ta shiga cikin al'amarin, ta na taimakawa wajen kokarin kamo wasu mutum biyu, namiji da mace, wadanda aka tabbatar da cewa su ne su ka saki bidiyon a gari bayan sun jima su na cutar Maryam tare da yi mata barazana.

A cewar Kwalle, a tsawon shekaru uku da su ka gabata matasan biyu sun dinga karbar kudi a hannun jarumar a bisa tsoratarwar cewa idan ta hana su kudin za su saki bidiyon duniya ta gani.

Kwalle ya ce, "To gaskiya wannan abu ne da ya shafi rayuwar ta, ba na harkar fim ba ne.

"Amma abin da mu ka bincika mu ka samu labari shi ne wannan abin ya faru ne kusan shekaru uku da su ka wuce.

"Kuma yaran da su ka yi abin sun yi ta yi mata barazana da shi, kan ta ba su kudi, idan ba haka ba za su saki bidiyo din, kuma a kan haka sun karbi kudi masu yawan gaske a wajen ta don gudun kada abin ya bayyana.

"To a shekaran jiya Laraba ne daya daga cikin su ya ce ta ba shi kudi zai kai mahaifiyar sa asibiti, ita kuma ta ce ba ta da kuɗi kuma ta gaji da ba su kudin.

"Don haka ganin ba su samu kudin ba su ka saki bidiyon.

"Kuma akwai shaida ta banki yadda ta rinka tura masu duk abin da su ka nema a wajen ta, don haka ana nan yanzu ana bin hanyar da za a kama su."

Shi kuwa sakataren kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta kasa (MOPPAN), reshen Jihar Kano, Malam Salisu Muhammad Officer, ya ce, "Mun san da maganar, amma mu a matsayin mu na shugabannin harkar fim babu wani abu da za mu ce. Kawai abu ne da ya shafe ta, ba harkar fim ba."

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sama da guda 100 sun kai hari garuruwan Neja

A yanzu haka dai an bayyana cewa wadanda ake zargi da sakin bidiyon sun yi batan dabo, jami'an tsaro na neman su ruwa a jallo.

Wata kawar Maryam Booth ta fada wa mujallar Fim cewa al'amarin ya girgiza jarumar matuka, har ta yi ta kuka domin bakin ciki "kan wannan cin amana da aka yi mata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel