June 12: Tinubu Ya Ce a Caccake Shi, Amma Ya Fadi Abin da ba Ya So a Yi
- Shugaba Bola Tinubu ya bukaci kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin fararen hula da kada su yanke tsammani wajen samun cigaba a Najeriya
- Ya bayyana haka ne game da yadda ake sukar gwamnatinsa, inda ya ce kada caccakar da ake masa ta zama sanadin yanke kauna
- Bola Tinubu ya sanar da haka ne a wani jawabi da aka watsa a talabijin domin bikin ranar dimokuraɗiyya ta bana a ranar Juma’a a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da ƙarfafa dimokuraɗiyya, yana mai cewa ƙasar ta yi shekara 27 tana kan tsarin tun daga ranar 29 ga Mayu, 1999.
A jawabin da ya yi na ranar dimokuraɗiyya, shugaban ya ce ‘yan Najeriya sun zaɓi shugabanninsu ta hanyar zaɓe, sun shaida mika mulki cikin lumana kuma sun warware sabani a kotuna da majalisun dokoki ba ta hanyar tashin hankali ba.

Source: Facebook
Fadar shugaban kasa ta wallafa cewa Bola Tinubu ya yi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da fatan samun nasara duk da kalubalen da suke fuskanta.
Tinubu ya ce a cacceke shi
A bayanin da ya yi, shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa suka da caccaka da 'yan kasa ke yi ba laifi ba ne, sai dai ba ya son hakan ya kai ga yake kauna ga samun cigaba mai dorewa.
Sanarwar fadar shugaban kasa ta nuna cewa ya ce:
“Ga majalisar dokoki ta kasa, bangaren shari’a, kafafen yaɗa Labarai da kungiyoyin fararen hula, ku ne masu kare jamhuriyarmu. Ku soke ni, ku yi sabani da ni, amma kada ku taɓa 'yanke kauna da samun cigaban Najeriya."

Source: Facebook
Kiran Tinubu ga 'yan Najeriya
Shugaban kasar ya yi magana game da 'yan Najeriya ya kuma yaba masu bisa gudunmuwar da suke bayarwa, musamman matasa, sarakuna da jami'an tsaro.

Kara karanta wannan
'Tinubu ya dawo da zaman lafiya a wasu yankuna': Matawalle ya hango nasara a 2027
Ya ce:
“Ga matasanmu, Najeriya ita ce kasar ku kuma makomarku. Ku gina ta, ku yi aiki a nan kuma ku kaɗa ƙuri’a a nan.
"Kowace babbar ƙasa mutanen da suka zauna a cikinta ne suka magance matsalolin ta suka gina ta, ba waɗanda suka bar cikinta ba.
“Ga dakarunmu, ‘yan sanda da jami’an leƙen asiri, Najeriya ta yaba da sadaukarwarku.
"Ga sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da shugabannin al’umma: na gode da goyon bayan da kuke bayarwa wajen samar da zaman lafiya da sulhu. Gwamnati ba za ta iya yin komai ita kaɗai ba."
Ga bidiyon Bola Tinubu da Channels TV ta wallafa a X:
Maganar Tinubu kan haraji
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kiraga 'yan dukkan Najeriya da su rika biyan haraji yadda ya kamata.
Bola Tinubu ya bayyana cewa ta hanyar biyan haraji ne kawai kasar za ta samu damar shimfida ayyukan cigaba a fannoni da dama.
Ya fadi haka ne ta bakin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima a wajen taron kaddamar da wani titi a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng
