Kotu ta ba El-Zakzaky damar ganin likitansa

Kotu ta ba El-Zakzaky damar ganin likitansa

Babbar kotun Kaduna, ta ba Shugaban kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi na Shi’a, Sheikh Ibrahim el-Zakzaky da matarsa, Zeenat, damar ganin Likitocin su don su sami damar iya bayyana a gaban kotun a zamanta na gaba.

Kotun ta sanya ranar 24 da 25 ga watan Fabrairu, domin ci gaba da sauraron shari’ar tasu. Ana dai zargin Zakzaky da matarsa Zeenat, da laifin kisan kai, yin taro ba tare da izini ba da kuma tayar da zaune tsaye da dai sauran wasu tuhume-tuhume.

A zaman kotun na jiya Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, Lauyan Zakzaky da matar tasa, Zeenat, Mista Femi Falana (SAN), ya shaida wa kotun cewa wadanda yake karewa ba su a cikin kotun ne a sakamkon hali na rashin lafiya.

Alkalin kotun, mai shari’a Gideon Kurada, sai ya dage sauraron shari’ar domin ba wadanda ake tuhumar damar bayyana a gaban kotun.

Kotu ta ba El-Zakzaky damar ganin likitansa
Kotu ta ba El-Zakzaky damar ganin likitansa
Asali: Facebook

A lokacin da Falana yake zantawa da manema labarai a bayan zaman kotun, ya bayyana cewa mai shari’a Kurada ya baiwa wadanda yake karewar damar ganin Likitocin su ne domin su sami damar bayyana a gaban kotun a zama na gaba.

Ya kuma ce, kotun ta bayar da damar yin gyara a kan tuhume-tuhumen da masu gabatar da kara suka gabatar domin su dace da mutanan biyu da ake tuhuma wadanda ba su a kotun.

Falana ya bayar da tabbacin cewa wadanda yake karewar za su bayyana a kotun a zaman kotun na gaba, ya ce Lauyoyin masu qara ba su ji dadin yanda jami’an tsaro suke kulle garin Kaduna ba a duk lokacin da ake yin shari’ar.

KU KARANTA KUMA: Mambobin jam’iyyun ADC da ZLP sama da 5,000 sun koma APC a Oyo

Shi kuma Mista Dari Bayero, jagoran Lauyoyin Gwamnatin Jihar Kaduna, ya shaida wa manema labarai cewa su a shirye suke domin yin shari’ar tare da dukkanin shaidun da za su bayar da shaida a gaban kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel