Ba zan goyi bayan Buhari ba idan zai sake zarcewa a karo na uku - Shekarau

Ba zan goyi bayan Buhari ba idan zai sake zarcewa a karo na uku - Shekarau

- Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ba zai goya wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya ba idan har ya nemi zarcewa a karo na uku

- Sai dai Shekarau ya ce ba ya tunanin shugaba Buhari zai nemi yin tazarce domin kaunar da ya ke yi wa mulkin damokradiyya

- Ya ce idan har Buhari zai nemi yin tazarce shakka babu kasar za ta riski kanta a cikin fitina

Tsohon gwamnan jahar Kano kuma dan majalisar dokokin tarayya, Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ba zai mara wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya ba idan har ya nemi zarcewa a karo na uku.

Shugaban kasar dai ya sha karyata zargin da wasu ke yi musamman daga jam’iyyar adawa cewa yana neman a yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima saboda ya samu ya kara Shugabancin kasar a karo na uku.

Ba zan goyi bayan Buhari ba idan zai sake zarcewa a karo na uku - Shekarau
Ba zan goyi bayan Buhari ba idan zai sake zarcewa a karo na uku - Shekarau
Asali: Depositphotos

Shekarau a wata hira da ya yi da shafin BBC game da kudirin da majalisar dattawa ya amince da shi na yin kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar, ya ce ba ya tunanin Buhari zai nemi yin tazarce domin kaunar da ya ke yi wa mulkin damokradiyya.

KU KARANTA KUMA: Mambobin jam’iyyun ADC da ZLP sama da 5,000 sun koma APC a Oyo

Ya bukaci al’umman kasar da su kyautata zatonsu kan Shugaba Buhari; yana mai cewa “yadda nake kyautata wa Buhari zato ko da na kusa dashi sun kawo wannan batu, a tunanina ba na jin zai yarda da batunsu”.

A cewarsa idan har Buhari zai nemi yin tazarce shakka babu za ta riski kanta a cikin fitina.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Buhari na ganawa da wata tawagar 'yan siyasa da shugabanni al'umma daga Kano da suka kai masa ziyara a fadar Aso Rock karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa; Sanata Kabiru Gaya suna daga cikin 'yan Majalisar Tarayya da Sarakuna da ke cikin tawagar. Kawo yanzu dai ba a san takamamen dalilin da yasa gwamnan da tawagarsa suka kai wa shugaban kasar ziyarar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel