'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Neja, an Kashe Mutane da Kona Gidaje

'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Neja, an Kashe Mutane da Kona Gidaje

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addancin da ya yi sanadiyyar hallaka mutanen da ba su san sauka ba a jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta tabbatar da cewa an hallaka mutane uku tare da kona gidaje yayin harin da 'yan bindigan suka kai a karamar hukumar Borgu
  • Hakazalika, rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa dakarun sojoji sun yi artabu da 'yan bindigan da suka kawo harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Neja - Rundunar 'yan sanda ta jihar Neja ta tabbatar da kisan mutane uku da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka yi.

'Yan bindigan dauke da makamai sun kashe mutanen ne a ƙauyen Pissa da ke karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa fadar sarki da dare, sun bindige matarsa bayan garkuwa da shi

'Yan bindiga sun kashe mutane a Neja
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana hakan a ranar Asabar, 13 ga watan Yunin 2026.

'Yan bindiga sun yi barna a Neja

SP Wasiu Abiodun ya bayyana cewa 'yan bindigan sun farmaki ƙauyen ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Ya ce an ƙona wasu gidaje a lokacin harin, sannan ya ƙara da cewa dakarun sojoji sun fafata da 'yan bindigan, sai dai babu cikakken bayani kan fafatawar da aka yi tsakaninsu.

“Rahoton da aka samu ya nuna cewa mutanen da ake zargin 'yan bindiga ne sun mamaye ƙauyen Pissa da ke karamar hukumar Borgu."
“An ruwaito cewa an kashe mutane uku a lokacin harin, sannan an ƙona wasu gidaje."
“Sai dai, dakarun sojoji sun mayar da martani kuma sun fafata da 'yan ta'addan, amma ƙarin bayani yana da ƙaranci a halin yanzu."

- SP Wasiu Abiodun

Kara karanta wannan

Mutane sun huta, jami'an tsaro sun yi ajalin hatsabibin dan bindiga, Baccujo

An yada jita-jita kan harin 'yan bindiga

Harin ya auku ne bayan da gwamnatin jiha da 'yan sanda suka ƙaryata rahoton yiwuwar kawo harin 'yan bindiga wanda ya sa 'yan makaranta a Minna, suka tashi daga makaranta cikin gaggawa kafin lokaci tare da tserewa zuwa gidajensu.

Daliban ba su jira lokacin tashi ba kafin su tsere saboda fargabar cewa 'yan bindiga na iya ƙaddamar da hari a makarantunsu.

Iyayen yara da suka ji labarin yiwuwar mamaye birnin Minna da 'yan ta'adda za su yi, sun bugawa shugabannin makarantun 'ya'yansu waya domin tabbatar da gaskiyar jita-jitar da kuma ko an rufe makarantu a ranar.

'Yan bindiga sun yi kisa a Neja
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kashe mutane a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu hatsabiban 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka aƙalla mutane 20 a wani mummunan hari da suka kai a jihar Kebbi.

Tantiran 'yan bindigan sun kashe mutanen ne a wani hari da suka kai a garin Fesken Rafi da ke karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi.

Gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana alhini game da harin na 'yan bindiga, wanda ta bayyana a matsayin abin takaici, sannan ta mika saƙon ta'aziyya ga iyalai da mazauna garin da abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com