Hankula sun tashi a Iyana Ipaja yayinda masu zanga-zanga suka yi gaba-da-gaba da jami’an tsaro

Hankula sun tashi a Iyana Ipaja yayinda masu zanga-zanga suka yi gaba-da-gaba da jami’an tsaro

- An shiga halin dar-dar a yankunan Aboru da Iyana Ipaja na jihar Lagas yayinda masu sana’ar tuka achaba ke zanga-zanga akan ayyukan wata kungiyar tsaro kan muhalli da sauran laifuffuka masu alaka

- Masu zanga-zangar na zargin rundunar da zarce iya hanyoyin da aka sanya haramci kan achaba

A yanzu haka, hankula na nan sun tashi a yankunan Aboru da Iyana Ipaja na jihar Lagas yayinda masu sana’ar tuka achaba ke zanga-zanga akan ayyukan wata kungiyar tsaro kan muhalli da sauran laifuffuka masu alaka.

Masu zanga-zangar wadanda suka toshe hanayar da taya sanye da wuta na zargin rundunar da zarce iya hanyoyin da aka sanya haramci kan achaba.

Hankula sun tashi a Iyana Ipaja yayinda masu zanga-zanga suka yi gaba-da-gaba da jami’an tsaro
Hankula sun tashi a Iyana Ipaja yayinda masu zanga-zanga suka yi gaba-da-gaba da jami’an tsaro
Asali: UGC

Idan za ku tuna, a aya mun ji cewa masu yan achaba da matukan Keke Napep da akafi sani da 'a daidaita sahu' sun gudanar da zanga-zanga a unguwar Ijora ta jihar Legas ranar Litinin kan dokar hana aikin babur da Keke Napep a jihar.

An samu labarin cewa an fara takaddama ne lokacin da yan sanda sukayi kokarin hana su zanga-zangar.

Yayinda suka kaddamar da zanga-zangar misalin karfe 8:21 na safe, yan babur da yan Keke Napep sun tare hanyoyi suna kona tayoyin mota.

Rahoton The Nation ya nuna cewa an bindige mutane uku a yanzu kuma matasa sun tare hanya.

Har ila yau a gefe daya mun ji cewa ayan dabbaka sabuwar dokar haramta amfani da babur da keke-napep a wasu Yankunan Legas, jami’an tsaro sun damke wadanda su ka sabawa doka.

KU KARANTA KUMA: Sufeto Janar na yan sanda ya gurfana a gaban majalisar dattawa kan rashin tsaro

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa bayan shigo da wannan doka ta hana Acaba, ‘Yan Sanda sun kama mutane 40, tare da rika abubuwan hawan. Babura 188 ne su ka shiga hannun ‘Yan Sanda a Legas.

Bayan haka an karbe keke-napep a sakamakon haramta amfani da su a wasu wurare a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel