Innalillahi wa inna ilaihir raji'un: Allah ya yi wa mahaifiyar Halima Atete rasuwa
- Mahaifiyar jarumar Kannywood, Halima Atete ta rasu
- Hajiya Maryam Yusuf ta amsa kiran mahaliccinta a safiyar yau Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, a wani asibitin Abuja bayan ta sha fama da jinya na tsawon lokaci
- Za a yi jana’izar ta a babban masallacin birnin tarayya Abuja
Rahoton da ke zuwa mana a yanzu ya nuna cewa Allah ya yiwa mahaifiyar fitacciyar jarumar nan ya Kanywood, Halima Atete rasuwa.
Mahaifiyar jarumar mai suna Hajiya Maryam Yusuf ta amsa kiran mahaliccinta a safiyar yau Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, a wani asibitin Abuja bayan ta sha fama da jinya na tsawon lokaci.
KU KARANTA KUMA: Kano: An samu gawar wani saurayi da budurwa tsirara cikin wani gida
Mujallar Fim ta ruwaito cewa za a yi jana’izar ta a babban masallacin birnin tarayya Abuja.
A gefe guda kuma mun ji cewa Shahararren tauraro a masana’antar shirya fina finan Hausa ta Kannywood, Sani Musa Danja ya zargi gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da rufe wani sabon kamfaninsa saboda bambancin siyasa dake tsakaninsu.
BBC Hausa ta ruwaito Danja ya zargi gwamnatin Ganduje ta hannun hukumar tace fina fina a jahar Kano ta rufe masa kamfanin da ya bude na daukan hotuna saboda siyasa, sai dai hukumar ta musanta wannan zargi, inda tace jarumin bai yi ma kamfaninsa rajista ba.
Tun ba yau ba, Sani Danja ya yi suna wajen goyon bayan jam’iyyar PDP da kuma tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, don haka baya tare da jam’iyyar APC da Gwamna Ganduje.
Sani Danja ya tabbatar da cewa ya yi rijista da dukkan hukumomin da ke kula da harkokin kasuwanci kafin kamfanin daukar hoton ya fara aiki, daga ciki har da hukumar rijstar harkokin kasuwanci ta Najeriya, Corporate Affairs Commissioin.
Sai dai shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Malam Isma'ila Na'abba Afakallah ya bayyana cewa babu wata makarkashiyar siyasa game da rufe kamfanin Sani Dan, yana mai cewa rashin yin rijista ne.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng