Mambobin jam’iyyun ADC da ZLP sama da 5,000 sun koma APC a Oyo
Koda dai an kammala zaben kasa kuma akwai sauran lokaci sosai kafin a sake wani zabe na gaba, har yanzu lamuran siyasa na daga cikin manyan batutuwan da ake tattaunawa yayinda yan siyasa ke bin hanyoyin kafa kansu don cimma aniyarsu.
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta sha kashi hannun jam’iyyar People Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan Oyo na 2019 bayan shekaru takwas da ta yi a mulki.
Watanni bayan nan, sai gashi APC ta koyi darasi yayinda ta fara sake karban tsoffi da sabbi mambobi yunkuri na sake habbaka karfinta gabannin zabe na gaba.
A ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, APC ta yi babban kamu yayinda ta tarbi masu sauya sheka sama da 5,000 daga jam’iyyun Zenith Labour Party (ZLP) da African Democratic Congress (ADC) a karamar hukumar Ibadan ta kudu maso yamma.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa masu sauya shekar sun samu jagorancin wani tsohon kwamishina a jihar, Cif Olowo Obisesan.
Legit.ng ta tattaro cewa akwai sunayen manyan mutane cikin jerin wadanda suka sauya shekar. Sun samu tarba daga Shugaban APC a yankin, Segun Oni.
“Wahalar da muke sha a siyasa ya isa hakan nan kuma muna bukatar cin moriyar damokradiyya,” in ji Shugaban ZLP na yanki, Sakiru Anifowose.
KU KARANTA KUMA: Sarkin Rano ya nada Nura trekker a matsayin 'Sarkin Zumuncin Rano'
Jimoh Rasidi Akanmu wanda ya kuma kasance Shugaban ADC ya jagoranci akalla mambobin jam’iyyar 3,000 zuwa APC.
A halin da ake ciki, mun ji cewa hukumar gudanar da zaben kasa INEC ta zabi ranar 19 ga Satumba 2020 domin gudanar da zaben gwamnan jihar Edo kuma 10 ga Oktoba domin gudanar da zaben jihar Ondo.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 6 ga Febriaru, 2020 a Abuja.
A cewar Mahmoud wa'adin gwamonin Edo da Ondo zasu kare a ranar 12 ga Nuwamba 2020 da 24 ga Febrairu 2020.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng