Musulmai Sun Yi Martani da Ake Alakanta Addinin da Ta’addanci da Sace Mutane
- Kungiyar Musulmi ta FASON ta yi karin haske game da yadda ake alaƙanta addinin Musulunci da ta'addanci da kuma garkuwa da mutane
- Shugaban FASON, Sheikh Tajudeen Abdul-Kareem, ya yi Allah wadai da sace dalibai da malamai 46 a Oyo tare da kira ga a kubutar da su
- Kungiyar ta bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su kawo karshen rashin tsaro tare da daina danganta laifuffuka da Musulmi ko Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Kungiyar Federation of Ahlus-Sunnah Organizations in Nigeria (FASON) ta wanke zargin da ake yiwa Musulmi.
Ƙungiyar Musulmin ta bayyana cewa addinin Musulunci ba shi da wata alaka da ta'addanci, fashi daji, garkuwa da mutane ko wasu ayyukan ta'asa.

Source: Facebook
Shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Tajudeen Abdul-Kareem wanda aka fi sani da Baba Lagbeni, ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka gudanar a Ibadan, cewar Leadership.
An soki masu alakanta Musulunci da ta'addanci
Kungiyar ta ce duk wanda ya yi imani da koyarwa da ka'idojin Musulunci na hakika ba zai aikata wani nau'in laifi ba kan mutum, kungiya ko al'umma.
Ya ce taron ya zama dole ne saboda sace dalibai 39 da malamai bakwai da aka yi a Oyo da kuma kalaman batanci da ake yi wa Musulunci.
Abdul-Kareem ya jaddada cewa dukkan miyagun ayyukan da 'yan bindiga, 'yan ta'adda ko wasu kungiyoyi ke aikatawa ba su da tushe a addinin Musulunci.
Ya ce ya ambaci ayar Alkur'ani mai tsarki ta Suratul Ma'idah domin nuna hukuncin da addini ya tanada kan ta'addanci da sauran miyagun dabi'u.
Har ila yau, ya kara da cewa masu danganta Musulunci da ta'addanci ko wasu laifuka makiyan Musulunci ne da kuma al'ummar Musulmi baki daya.

Source: Original
Addu'o'in da kungiyar ta yi kan tsaro
Abdul-Kareem ya ce mambobin kungiyar sun shafe sama da mako suna addu'ar samun nasarar kubutar da dalibai 39 da malamai bakwai da aka sace.
Ya yi Allah wadai da sace mutanen da aka yi a karamar hukumar Oriire ta Oyo, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Har ila yau, ya ce wannan taron manema labarai ya mayar da hankali kan matsalolin da kasa ke fuskanta, musamman batun sace dalibai da malamai a Oyo.
A cewarsa, suna kuma addu'ar samun zaman lafiya a Najeriya da duniya baki daya, domin ba sa son yaki ko rikici, cewar Daily Post.
Ya gargadi 'yan bindiga da su daina ayyukansu saboda babu lada a duniya ko lahira cikin irin wadannan munanan laifuffuka.
Shari'ar Musulunci: Musulmi sun soki yan bindiga
Mun ba ku labarin cewa wata kungiyar Musulmi ta yi Allah-wadai da masu garkuwa da mutane da suka bukaci sai an kafa shari'ar Musulunci saboda bukatunsu.
Kungiyar ta caccaki maharan tana mai cewa ba su wakiltar Musulunci ko Musulmai ko ta wani hanya saboda laifuffukansu.
Bayan sace dalibai 39 da malamai bakwai tare da kashe mutum biyu a Oriire, kungiyar ta jaddada cewa Musulunci ya haramta ta’addanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

