Gwamnan Borno ya kwana 2 a Monguno don daura harsashin gina gidajen 'yan gudun hijira

Gwamnan Borno ya kwana 2 a Monguno don daura harsashin gina gidajen 'yan gudun hijira

- Gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci yankin Monguno inda ya kwashe tsawon kwana biyu a garin

- A yayin ziyarar, gwamnan yadaura harsashin ginin gidaje 1,000 saboda 'yan gudun hijira da suka yada zango a makarantu

- Zulum ya kuma daura harsashin ginin makarantar Islamiyya wadda za ta samar wa da mutane 10,000 da ke da ilimin addinin Musulunci damar samun difloma a ilimin zamani

Gwamna Babagana Umara Zulum na jahar Borno, ya ziyarci yankin Monguno inda ya kwashe tsawon kwana biyu a garin.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi daga hadimin gwamnan kan harkokin labarai, Isa Gusau ya fitar a ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairu, shafin BBC ta ruwaito.

A yayin ziyarar, gwamnan yadaura harsashin ginin gidaje 1,000 saboda 'yan gudun hijira da suka yada zango a makarantu.

Gwamnan ya kuma daura harsashin ginin makarantar Islamiyya wadda za ta samar wa da mutane 10,000 da ke da ilimin addinin Musulunci damar samun difloma a ilimin zamani.

An tattaro cewa akwai 'yan gudun hijra 89,000 da ke zaune a Monguno wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

Kwamishinan sake gina Borno, Injiniya Mustapha Gubio ya ce an iza harsashin gina rukunin gidajen domin samar wa 'yan gudun hijrar wajen zama.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Sufeto Janar na yan sanda ya fada ma gwamnoni 36 abunda ya kamata su yi

Ya ce hakan zai bai wa makarantun da 'yan gudun hijrar suka mamaye damar komawa bakin aiki.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ce yana shirin gina wani katafaren filin wasanni mai girmar irin wanda ake amfani da shi a wasannin kasashen duniya (Olympic) a babban birnin jihar domin inganta cigaban wasanni.

Mai magana da yawun gwamnan, Muhammad Bello, ya ce Tambuwal ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba lokacin da ya kai ziyarar bazata wurin da ake ginin filin wasanni na tunawa da Giginya a Sokoto da ake shirin gudanar da wasannin kwallon hannu na kasa na 'yan kasa da shekaru 12 da 15.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel