Rashin tsaro: Sufeto Janar na yan sanda ya fada ma gwamnoni 36 abunda ya kamata su yi

Rashin tsaro: Sufeto Janar na yan sanda ya fada ma gwamnoni 36 abunda ya kamata su yi

- Sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya bukaci gwamnonin jahohi da su sauke hakkin da ya rataya a wuyansu

- Ya ce wadanda ke aikata laifuffuka na da dalilansu na aikata hakan, kama daga rashin aikin yi, rashin ilimi da sauran abubuwa da ya kamata gwamnati ta sauke

- Adamu ya ce yayinda al’umma ke taimakawa wajen gano laifi, yan sanda Za su taimaka masu wajen magance shi

Biyo bayan zantawar da ya yi da sanatoci a jiya Laraba, 5 ga watan Janairu kan lamuran tsaro, sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu, ya bukaci gwamnonin jahohi da su sauke hakkin da ya rataya a wuyansu, cewa wadanda ke aikata laifuffuka na da dalilansu na aikata hakan.

Shugaban yan sandan ya kasance a majalisar dattawan domin kora wa yan Majalisar jawabai kan manufar yan sanda na jiha.

Rashin tsaro: Sufeto Janar na yan sanda ya fada ma gwamnoni 36 abunda ya kamata su yi
Rashin tsaro: Sufeto Janar na yan sanda ya fada ma gwamnoni 36 abunda ya kamata su yi
Asali: Twitter

Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, sufeton yan sandan ya ce: “idan rashin aikin yi ne, idan rashin ilimi ne ko wasu lamura da ke bukatar gwamnati ta shiga lanarin, ya kamata gamnoni su dauki wannan nauyi, shugaban kananan hukumomi su dauki wannan nauyi. Ba wai a barwa hukumomin tsaro komai ba su kadai.”

Ya bayyana cewa akwai shirye-shiryen mayar da yan sanda zuwa garuruwa.

Adamu ya ce yayinda al’umma ke taimakawa wajen gano laifi, yan sanda Za su taimaka masu wajen magance shi.

KU KARANTA KUMA: Al-Mustapha: Sharri ake yi wa Abacha, ni ma an nemi in yi wa Buhari kazafi

Shugaban Majalisar dattawa, Ahmad Lawan, bayan taron, ya ce: “rundunar yan sandan ya ce ya zama dole a nemo hanyar mafi inganci don kare rayuka da jama’a”.

A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta sanar da cewa ta kubutar da mutane 26 da masu garkuwa da mutane a Dugun Muazu da ke karamar hukumar Sabuwa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Gambo Isah, shine ya sanar da hakan yayin wani taro da manema labarai da ya kira ranar Laraba a Katsina.

Isah, mai mukamin SP, ya sanar da cewa akwai Mata 8 da Maza 18 daga cikin mutanen da suka kubutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel